RECENT UPDATES
[···] 50 · February 15, 2018

SHIRIN HANCIN GAUTA DAGA 2013 ZUWA 2017 Shirin hancin Gauta shirin da Rahama Radio Kano take kawowa a duk watan Ramadhan shirin da Dr. Abdulkadir Isma’il da kuma Dr. Aminu Isma’il suke gabatarwa, Game da shirin: Shiri ne da yake tattauna batutuwan da suka shafi rayuwa da zaman takewar musulmai ba don komai ba sai don ayi gyara ko neman masalaha ga wasu, shirin yakan haskawa al’umma irin kalubalen da yake gaban al’ummar musulmai, irin hanyoyin da ake bi wajen yakar musulmai yaki da kwa-kwalwa ba yaki da makami ba, abubuwan da muke yi wanda bama musan me suke nufi ba, kari kan dadi warware shubuhohi kamar batun idan mutum zai yi karatun Addini to sai ya hakura da na boko, idan kuma zai yi na boko sai ya hakura da na Addini, war-ware karerayin dake jingina musulunci da musulmai da rashin wayewa, kai abin ma ba zan iya kwatantawa ba kai dai kawai sai ka saurara na san zaka bada labari, Duba da irin amfanin da wannan shiri ke dashi da tasirin da yayi wajen wayar da kan al’ummar jihar nan ta Kano ya sa cibiyar Darulfikr.com ta tattaro shirin tun daga shekarar 2013 zuwa wannan shekarar ta 2017 domin jama’ar da basu samu damar saurara ba da kuma wadanda basa jihar Kano suma su samu damar amfana da wannan shiri, ba don komai ba sai don mu gudu tare mu kuma tsira tare, Kar na cikaku da surutu domin yin downloading kana iya bin wadannan links dake kasa: 1. Complete Hancin gauta 2013 https://goo.gl/zd86gz 2. Complete Hancin gauta 2014 https://goo.gl/XuYkJg 3. Complete Hancin gauta 2015 https://goo.gl/omp2YL 4. Complete Hancin gauta 2016 https://goo.gl/fWtsjg 5. Complete Hancin gauta 2017 https://goo.gl/4wQsbz 6. Complete Hancin gauta na Shekarun gabaki daya https://goo.gl/WUgghB Ayi sauraro lfy, Darulfikr.com taku ce domin yada Sunnah Basheer Journalist Sharfadi Faisal Nasir Muhd Muhd Basheer Ridwan Ammar Isah Nuhu Mustapha bin Adam Hassan,Hussaini Auwalu Ya’u Muhd Habib Adam Jami’an da suka agaza wajen kawo muku wadannan shirye – shirye, #BasheerSharfadi

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 781 · July 07, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853