IZALA: MARAYU 350 SUN SAMU KAYAN SALLAH

December 31, 1969

JIBWIS Central Mosque Biu, Borno State

JIBWIS BIU, BORNO STATE Kimanin Marayu Dari uku da hamsin (350) ne ayau suka samu kayakin sallah karkashin jagorancin Kungiyar JAMA'ATU IZALATUL- BID'AH WA IQAMATIS-SUNNAH reshen Jahar Borno Karamar hukumar Biu karkashin Committee na Marayu. shugaban kwamittee Alh Muhammad Imam (Ya Shehu) *ya umurci marayu da su kama Sana'a domin koyan yadda ake dogaro da kai * Ya kuma tabbatar musu da cewar dukkan wani maraya da yake fama da jinya to a tabbar ankaishi Asibitinsa mai Suna "Imam Memorial" sabida ya cire wa kowani maraya kashi hamsin 50% daga cikin kudin jinyarsa. * Tuni akwai wasu Marayu wadanda aka dauke musu kudin makarantunsu. *Ya kuma mika godiyarsa zuwaga sauran membobi na wannan kwamitee kamar su: 1. Malam Inuwa 2. Alh Umar 3. Alh Hashimu 4. Alh Yusuf Chairman 5, Alh Sani Tela 6. Malam Khidir Alh Adam 7. Malam Shu'aibu Bala 8. Malam dahiru Da sauran wadanda bazai iya tuna sunayensuba * Ya kuma shaidawa marayun cewa bashine kadai abunda ake shirya musu Ba akwai kuduri da ake yiwa marayun Wanda Inshaa Allahu ana son kowani maraya ya koyi san'a mai kyau kuma yayi karatu sosai domin shima ya taimakawa Yan uwansa musulmi. * Akarshe Ya Shehu ya yi kiraga masu wannu da shuni da su cigaba da taimakawa marayun. *Secretary na Qugiya Alh Bukar Kadafur ya nuna farin cikinsa da fatan alkhairi ga wannan committee mai albarka. wannan ya biyo bayan wani Ziyara Wanda kungiyar ta kai a gidan yari da ke garin Biu kana Kungiyar ta tura Malamai zuwa kauyukan Biu da kuma cikin Garin domin gudanar da tafsirin Al-Qur'an Mai Girma na watan Ramadan na bana 1437/2016 Wanda a kimani qungiyar ta kashe kudi kamanin naira dubu Dari biyar (N500,000) qungiyar dai karkashin jagorancin Shugaba Alh Umar Yamele da Secretaransa Alh Bukar Kadafur da kuma shugaban Majlisar Malamai Sheikh Zakariyya Isa Sa'eed Biu sun bayyanawa Jama'a cewa babban burinsu a yanxu shine hadin kan musulmi. Harwa yau Sheikh Ya yi addu'ar Neman zaman lafiya a garuruwar musulmi. JIBWIS SOCIAL MEDIA BIU, BORNO STATE 21/09/1437 ::::26/06/2016

by: Mai Umar Isa Biu · 794 · June 26, 2016

UPCOMING EVENTS

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853