WACECE MACE GANGARIYA?

January 31, 2016

Mambayya House, Gwammaja, Kano

Rayuwa sai da kulawa! Ya 'yar uwata mai albarka, shin me kika tanadarwa furannin gidanki masu kamshi da haskaka sansani wato yaya mata? A lokuta mafiya tsada a rayuwarsu! Wato lokacin balaga da lokacin shiga daki a matsayin baquwar gidan aure Idan tun da fari kin rigayi zukatansu da alkhayri tun gabanin shigar sharri da shashanci Cibiyar bincike da wayar da kan mata ta DAKE AKE CONSULTANCY (wato Taskar Alheri) ta sake dakakowa, don gabatar da taronta mai taken; "TSARABAR MATAN DA NI'IMARSU BATA QAREWA" Bayanai ne da masana zasu aike dashi matattarar tunani, kuma na'ura mai sarrafa hankula wato zuciya! Don kunna fitulun da zasu haskaka gaba da bayan rayuwar 'yaya mata! Da yiwa rayuwar aure kwalliya da sinadarai kyawawa Wacce zata gabatar da takarda ta farko; Hadiza Balanti Chediyar 'Yan Gurasa Taken takardarta; "WACECE MACE GANGARIYA?" Mai gabatar da takarda ta biyu; Hajiya Kaltume A.D Abubakar (KSSSSMB gidan malamai Kano). Taken takardarta; "TSARABAR 'YAMMATA MASU AJI" Mai gabatar da takarda ta uku, Malama Rabi Bello Fagge taken takardarta; "ASHE NIMA ZAN IYA?" Zaa gabatar wannan taro; RANA: Lahadi 31/01/2016 LOKACI: 9:00am WURI: Mambayya House, Gwammaja, Kano. Kudin shiga dubu daya (1,000) ne kachal! wani karin haske shine; Akwai rangwamen biyan kudin shiga, ga wadanda suka halarci taronmu na 01/11/15, da zarar kin nuna gate pass din da aka baki da kika biya kudi, dari biyar kadai zaki biya ki shiga. Taron yini daya ne tal! Kuma na mata zalla, daga shekarun balaga har tsufa! Zaku iya tuntubarmu akan wadannan lambobi: 0803 911 7047, 0812 222 8484, 0817 997 7373. Allah ya bada ikon halarta, amin!

by: Hadiza Balanti · 3,109 · January 11, 2016

UPCOMING EVENTS

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853