ALBSIHIRIN KU AHLUSSUNNAHN NIGERIA DAMA NA KETARE: ((SUNNAH TA SAMU GAGARUMAR KARUWA))

Jama’a Assalamu Alaikum, a yau muhimmin sako ne nake dauke dashi wanda gangamin gamayyar Matasan Ahlussunnah na wannan kasa suka bada sakon a isar gareku, Sunnah ce ta samu gagarumar karuwar a wannan saha na shafukan yanar gizo-gizo inda gamayyar matasan suka samar da wani qasaitaccen dandanli na musamman domin tunkarar tarin kalubalen dake fuskantar tafiyar sunnah a wannan saha. Nasan dai dukkannin ku na da masaniya kan wadancanan ka da suka taso tafiyar a gaba, ba don komai ba sai don ganin sun dabbaka addini irin na shaidan domin su ga cewa jama’ar mu sun rifta ciki bai daya, kuma dama dai tuntuni mun jima da karantawa a islamiya fadin Allah cewa: ((“ود كثير من أهل الكتاب لو يردونكم من بعد إيمانكم كفارا حسدا من عند أنفسهم من بعد ما تبين لهم الحق…”)) Dalilin wannan aya ya sanya matasan yin dogon nazari kan wannan yunkuri da mutanen can keyi na ganin cewa sun dagula mana al’amari ta yadda zamu zamo daya dasu kaga idan anje can ranar gobe kiyama alfaharin da Manzon tsira zai yi sai ya zama an ce babu mutanen mu, tunda dai sun biyewa mutanan da ma’aiki yace: “duk wanda yayi kama (koyi) da wasu mutanen to hakika yana daga cikin su” Shin ko wane yunkuri matasan su kayi wajen dakile wannan tuggu?? Daya daga cikin jagororin wannan tafiyar yayi min karin haske akai kamar haka: “Toh! Alhamdulillah, duba da halin da Ahlussunnah ke ciki a wannan dandali hakan yasa muka yi karamin yunkuri inda muka samar da sabon dandali wanda muke sa ran zai taimaka wajen dakile kalubalen da sunnah ke fuskanta sannan zamu yi amfani da shi wajen bayyanawa duniya halin da Sunnah da Ahlinta suke ciki anan Nigeria, wannan dandali wanda aka yiwa lakabi da Sunnah News Nigeria zai mayar da hankali wajen wadancan abubuwa, A gefe guda kuma yana da bangarori da dama kamar fatawoyi na malamai daban-daban, sanarwa, labarai, ingantaccen tarihi, rubututtuka na wayar da kai, da kuma mayar da martani na ilmi ga masu adawa da Sunnah tare da warware shubuhohi irin na masu mugunyar akidu dake yawaita a wannan lokaci, sannan akwai bangaren da muma Ahlussunnah zamu dinga bayyanawa duniya ra’ayoyin mu akan batutuwa daban-daban, Duba da yadda aka yi nisa wajen kwarewa a wadannan shafuka ya sanya muka yi amfani da hanyoyin da zamu saukakawa al’umma amfani da dandalin kamar haka: Shafin yana da Application na Android wanda idan ka sauke a wayar ka zaka dinga samun dukkan wasu bayanai ba tare da sai an ce ka shiga opera ka rubuta kaza ba, a’a kawai installing zaka yi, kana kunna data zaka dinga ganin sakonnin wannan dandali, Zaka iya yin downloading na application din ta hanyar bin wannan link din Darulfikr.com ko a sunnahnewsnigeria.wordpress.com Sannan akwai “Translator” da zaka iya canja shafin zuwa yaren da kake bukata, Zaka iya yin searching na wani abu da kake nema akan sa , Akwai inda zaka iya bin mu ta email idan ka sanya email dinka ka danna “follow” to duk sanda muka sanya sabon posting za’a tura maka ta email din ka, Sannan daga kan shafin idan ka ga abu yayi maka zaka iya danna alamar “share” ka tura shi zuwa Facebook, WhatsApp, Twitter da sauransu kai tsaye daga kan dandalin, Sannan zaku iya bibiyar mu ta kafofin Facebook da Twitter ta yadda muna yin posting zaku dinga samun sa, zaku iya samun mu ta adreshi kamar haka: Facebook: facebook.com/sunnahnigeria.ng (Sunnah News Nigeria) Twitter: twitter.com/sunnahnigeria Youtube: Hausa Online Media Zaku iya aiko mana da rahotanin halin da sunnah take ciki a yankunan ku ta hanyoyi kamar haka: Email: sunnahnewsnigeria@gm­ail.com Da kuma lambobin waya kamar haka: 09035830253, 08066989773, 08149342004, 0814­9332007. SUNNAH NEWS NIGERIA LABARAN SUNNAH A TAFIN HANNUN KU Jama’a karshen sakon nasu kenan da suka bani na isar muku, Basheer Journalist Sharfadi 24/11/2017 #SunnahNewsNigeria #Sunnah #Arewa

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 987 · November 24, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853