BABU MASU KASHE MASU JEFA KURI'A A RANAR ZABE SAI AZZALUMAI:

Muna tabbatar wa al'ummar Musulmin Duniya cewa babu wani nassi daga Alkur'ani da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah, da yake haramta jefa kuri'a saboda zaben Shugaban Kasa ko waninsa, haka nan babu wani nassi daga Alkur'ani ko Sunnah da yake haramta nada Shugaba ta hanyar jama'a masu rinjaye, haka nan babu wani nassi daga Alkur'ani ko Sunnah da ya halatta kashe masu jefa kuri'unsu saboda zaben wanda zai mulke su: shugaban Kasa, ko gwamna, ko wani dan majalisa. ************************ Sannan muna tabbatar wa Musulmin Duniya cewa Nassi da Ijmaa'i duk sun tabbata a kan halacci da kuma wajibcin yakar Khawaarijawa masu kashe dukkan wani da ya saba wa bidi'arsu da batarsu. Ga kadan daga cikin dalila:- 1. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 7/481 :- ((وان قتال الخوارج مما امر به صلى الله عليه وسلم ولذلك اتفق على قتالهم الصحابة والاءمة)). Ma'ana: ((Kalle yakar Khawaarijawa yana daga cikin abin da (Annabi) mai tsira da amincin Allah ya yi umurni da shi, wannan shi ne ma ya sa Sahabbai da sauran Shugabanni suka yi ittifaki a kan yakarsu)). 2. Imamu Muslim ya ruwaito Hadithi na 1066 daga babban Sahabi Aliyyu Bin Abii Taalib ya ce:- ((سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: سيخرج في اخر الزمان قوم احداث الأسنان سفهاء الأحلام يقولون من خير قول البرية يقرءون القران لا يجاوز حناجرهم يمرقون من الدين كما يمرق السهم من الرمية، فإذا لقيتموهم فاقتلوهم؛ فان في قتلهم اجرا لمن قتلهم عند الله يوم القيامة)). Ma'ana: ((Na ji Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana cewa: Da sannu a karshen zamani wasu mutane masu karancin shekaru, masu wautar tunani, suna fadin maganar Mafi alherin halitta, suna karanta Alkur'ani (amma) ba ya wuce makoshinsu, suna fita daga Addini kamar yadda kibiya take fita daga dabbar da aka harba, Idan kun gamu da su (a fagen gada) Ku kashe su; lalle cikin kisansu akwai wani irin lada a wurin Allah ranar Kiyamah ga duk wanda ya kashe su)). ********************************* Muna rokon Allah Ya dawo mana da zaman lafiya cikin wannan babbar Kasa tamu Nigeria, Ya kuma kare mu daga sharrin Khawaarijawa da sauran azzalumai jinsinsu. Ya ba mu damar yin zabubbukanmu lafiya Ya azurta mu da shugabannin kirki. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 222 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853