DUK ALHERIN DA GASKIYA BA TA KAWO SHI BA KARYA BA ZA TA KAWO SHI BA:

1. Lalle abin bakin ciki ne matuka wasu su bijire wa talakawansu, su bijire wa kasarsu, su yi magana da irin harshen khawaarijawan boko haram su watsa takardun da ke haramta wa talakawan Nigeria jefa kuri'a a ranakun zabuka masu zuwa! 2. Lalle abin bakin ciki ne matuka irin wadannan mutanen su sake bijire wa talkawansu, da kasarsu su sake rubuta wasu Kasidun karya da kage su jingina su ga shugabannin Addini suna masu cewa a cikin Kasidun: Kada wani Kirista ya zabi kowa sai da takaran da yake Kirista ne! Kada wani Musulmi ya zabi kowa sai dan takaran da yake Musulmi ne! ********************** Manufarsu da yin karyar farko ita ce: Idan har mutane suka ji tsoron fita su jefa kuri'a a irin wadannan jihohin da a ka rarraba wadannan sakonni karyar to hakan zai rage wa Jam'iyyar hamayya samun kuri'un da zai iya kai ta ga samun nasara a kansu. Sannan Manufarsu da yin karya ta biyu ita ce: Idan har dukkan Kirista suka jefa wa Dan takaransu kuri'a to hakan ko da bai ba wa Dan takararsu nasarar zaben ba, to kuwa zai hana Dan takarar jam'iyyar hamayya samun bayyananniyar nasara a idanun Duniya! **************************** Allah Ka raba mu da sharrin mara kishin Kasa da Al'umma, Ka ba wa kasarmu lafiya da zaman lafiya, Ka azurta mu da shugannin kwarai masu kishin Kasa da Al'umma. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 287 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853