TSAWAITAR LOKACIN MULKI KO GAJERTANSA BA SU DA ALAKA DA HALACCIN KO HARAMCIN MULKIN MAI YIN MULKI:

1. Ya kamata Musulmi su san cewa wani lokaci mulkin azzalumi ya kan tsawaita (dawwama) duk kuwa da yake Allah ba ya son irin wannan mulki so irin na Shari'ah, misalin haka shi ne irin yadda mulkin Fir'aunan zamanin Annabi Musa (watau Haksus na biyar) ya tsawaita inda ya kai shekaru 50 ko fiye da haka. Haka nan ya kamata Musulmi su san cewa wani lokaci kuma mulkin adilin mai mulki ya kan gajerta ya kasa tsawaita, misali a nan mulkin babban Taabi'i Umar Bin Abdul Aziz, tsawon mulkin wannan bawan Allah duk da yawan adalcinsa shekaru biyu ne kacal. Haka Sayyidina Abubkar As-Siddiq duk da yawan adalcinsa tsawon mulkinsa shekaru biyu ne da wata uku da yan kwanaki. Haka nan Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib duk da yawan adalcinsa amma tsawon mulkinsa shekaru biyar ne da wata shida kadai. 2. Ya kamata Musulmi su san cewa lafazin nan da ake yawan furtawa:- ((يدوم الملك مع الكفر ولا يدوم مع الظلم)) Ma'ana: ((Mulki na dawwama (tsawaita) tare da kafirci, amma ba ya dawwama tare da zalunci)) Ya kamata Musulmi su san cewa wannan lafazi ko kuwa lafazi mai kama da shi, ba nassin ayar Alkur'ani ba ne, ba kuma nassin Hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah ba ne, kuma babu wani Ijma'in da ya zo da tabbatar ma'anan shi wannan lafazi a dai iya sanina. 3. Ya kamata Musulmi su san cewa babbar hujja watau Ijmaa'i ya tabbata a kan cewa shugabanci a Shari'ance ba ya kulluwa ga kafiri. Ya zo cikin Ahkaamu Ahlizzimmah 2/687 kamar haka: ((قال ابن المنذر: اجمع كل من يحفظ عنه من أهل العلم ان الكافر لا ولاية له على المسلم بحال)). Ma'ana: ((Ibnul Munzir Ya ce: Dukkan wadanda ake haddar Ilmi daga garesu daga ma'abuta Ilmi sun yi Ijmaa'i a kan cewa Kafiri ba yi da hakkin jagoranci a kan Musulmi ta ko wani hali)). Sannan Imaamun Nawawii ya ce cikin Sharhu Sahihi Muslim 6/315:- ((وقال القاضي عياض: اجمع العلماء على ان الإمامة لا تنعقد لكافر)). Ma'ana: ((Qaadii Iyaadh ya ce: Maluma sun yi Ijmaa'i a kan cewa babban jagoranci ba ya kulluwa ga kafiri)). Sannan Al-Hafiz Ibnu Hajar ya ce cikin Fathul Baarii 13/123:- ((ينعزل بالكفر اجماعا)). Ma'ana: ((Yana tubuwa daga mulki saboda kafirci, a bisa Ijmaa'i)). Muna fata yan'uwa za su rika yin hattara da taka tsantsan cikin maganganu da za su rika furtawa. Allah Ya taimake Mu Ya dora mu bisa daidai cikin kudurinmu, da zantuttukanmu, da ayyukanmu. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 194 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853