DUKKAN ALHERI NA CIKIN KOYI DA ANNABI MUHAMMAD DUKKAN SHARRI NA CIKIN SABA AMSA

: Wajibi ne mu san cewa maganar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ita ce gaba da maganar kowa a duniyan nan komin girmansa a idanun jama'arsa. Babban Malamin Sunnah Alhafiz Ibnu Rajab wanda ya mutu a shekarar hijira ta 795 watau yau shekaru 640 ke nan da suka wuce, ya yi wa malamai wata maga da ya kamata a rubuta da ruwan zinari, ya ce cikin littafinsa mai suna Alhikamul Jadiratu Bil Iza'ah shafi na 12:- ((فالواجب على كل من بلغه امر الرسول صلى الله عليه وسلم وعرفه ان يبينه للامة وينصح لهم ويأمرهم باتباع أمره وان خالف ذلك رأي عظيم من الامة؛ فان امر رسول الله صلى الله عليه وسلم احق ان يعظم ويقتدى به من رأي اي معظم قد خالف أمره في بعض الاشياء خطا، ومن هنا رد الصحابة ومن بعدهم على كل مخالف سنة صحيحة، وربما اغلظوا في الرد لا بغضا له، بل هو محبوب عندهم معظم في نفوسهم، ولكن رسول الله احب اليهم وأمره فوق امر كل مخلوق، فإذا تعارض امر الرسول وأمر غيره فأمر الرسول اولى ان يقدم ويتبع ولا يمنع من ذلك تعظيم من خالف أمره وان كان مغفورا له، بل ذلك المخالف المغفور له لا يكره ان يخالف أمره اذا ظهر امر الرسول صلى الله عليه وسلم بخلافه)). انتهى. Ma'ana: ((wajibi ne a kan dukkan wanda umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya isa zuwa gare shi, ya kuma san shi, ya bayyana shi ga Al'ummah, ya musu nasiha, ya umurce su da bin umurninsa koda kuwa hakan ya saba wa ra'ayin wani babba a cikin Al'ummah, saboda umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah shi ya fi cancantar a girmama shi, kuma a yi koyi da shi a kan ra'ayin dukkan wani wanda ake girmamawa amma kuma umurninsa ya saba wa umurnin shi cikin sashin lamura cikin kure, wannan shi ya sa ma Sahabbai da wadanda suka biyo bayansu suka yi wa dukkan wanda ya saba wa Sahihiyar Sunnah raddi, wani lokaci ma raddi mai kaushi, ba wai kuma saboda suna nuna kiyayya ba ce gare shi, a'a yana nan abin so a gare su kuma abin girmamawa a cikin rayukansu, to amma Manzon Allah shi ne mafi soyuwa a gare su, sannan umurninsa shi yake sama da umurnin ko wace halitta. Saboda haka idan umurnin Manzon Allah ya yi karo da umurnin waninsa, to umurnin Manzon Allah shi ya fi cancantar a gabatar kuma a bi, wannan kuwa ba zai hana a girmama mutumin da ya saba wa umurnin Manzon Allah ba matukar dai ana gafarta wa kuren cikin Sahari'ah, kuma shi wannan da ya yi sabon cikin kure ba zai nuna kyamar a saba wa umurninsa matukar dai umurnin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya bayyana a matsayin mai saba masa)). ************************************* Sannan Sheik Uthmanu Dan Fodiyo ya yi wata magana mai kyawun gaske wacce za ta amfanar da masu wa'azi a cikin littafin Ihya'us Sunnah shafi na 8:- ((قد انعقد الإجماع على ان آراء المجتهدين كلها مسالك الى الجنة وطرق الى الخيرات فمن سلك منها طريقا وصله الى ما وصلوا اليه حقاً ومن عدل عنه قيل له سحقا! ويجوز تقليدهم في كل رأي الا ما خالف نص القران او نص الحديث او القواعد او القياس الجلي، فافهم)). انتهى. Ma'ana: ((Ijma'i ya kullu a kan cewa: dukkan ra'ayoyin Mujtahidai mashiga ce ta zuwa Aljanna, kuma hanyoyi ne na alkhairai, wanda duk ya bi wata hanya cikinsu tabbas za ta kai shi inda suka kai, wanda kuma ya baude ga barin su sai a ce da shi tir. Sannan yana halatta a yi koyi da su cikin ko wane ra'ayi, amma banda abin da ra'ayin da ya saba wa nassin Alkur'ani, ko nassin Hadithi, ko saba wa Ka'idodi, da Ijma'i, ko Kiyasi Jaliyyi, ka fahimta)). ********************************** Wannan yana wajabta cewa: Dukkan abin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi umurni da yin sa, to wajibi ne daliban ilmi su bayyanar da shi ga Al'ummah, sannan da za a samu wani mai son zuciya da zai yi kokarin hana su yin hakan to ba za su saurara masa ba, wannan shi ne daidai kuma shi ne hanyar Annabi da sauran Maluman Sunnah. Sannan haramun ne a kan kowane Musulmi ya bi ijtihadin wani malami komin girmansa matukar dai ijtihadin nasa ya saba wa nassin Alkur'ani, ko nassin Hadithi, ko nassin Ijma'i, ko Kiyasi Jaliyyi, kamar dai yadda Sheik Uthmanu Dan Fodiyo ya bayyana wa dukkan al'ummar Musulmi. Muna rokon Allah da Ya tabbatar da dugaduganmu a kan bin sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah. Ameen. DR IBRAHIM JALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 213 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853