A CIKIN MAZHABAR MALIKIYYAH DA MA KO WACE MAZHABA ANA IYA SAMUN ABIN DA ZAI SABA WA SAHIHIYAR SUNNAH:

Jahilci ne matuka wani yace duk wani abin da yake mashuuri ne cikin Mazhabar Malikiyyah ba zai yiwu ya saba wa wata sahihiyar Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ba, a gaskiya irin wannan aqiidar babban hadari ne ga imanin Musulmi. Ana iya fahimtar gaskiyar wannan magana tamu idan aka fahimci cewa dukkan shahararrun malumanmu na fiqhu sun gaya wa Duniya cewa idan suka yi wata magana sannan aka ga maganar tasu ta saba wa hadithin Annabi to a yi watsi da maganar tasu a Koma a yi riko da Sahihin hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah. Sannan maganar cewa mazhabar Malikiyyah tana iya saba wa sahihiyar Sunnah ba wai a mas'alar Sakin hannu ko dora su a kan kirji ba ne kawai take, a'a akwai ta ma cikin wasu mas'alolin daban. Misali:- Mas'alar daura laya, Hadithan Manzon Allah sun inganta cikin wannan mas'alar, kamar hadithin:- ((من تعلق تميمة فقد اشرك)). Ma'ana: ((Duk wanda ya rataya laya to hakika ya yi Shirka)). Da kuma hadithin:- ((ان الرقى والتمائم والتولة شرك)). Ma'ana: ((Lalle Tawaida-tawaida, da kuma Layu, da Abubuwan sanya soyayya ko kiyayya tsakanin namiji da mace, Shirka ce)). A nan Annabi bai banbance tsakanin laya da laya ba, a'a duk ya hada su ya yi hanin a rataya su. Kuma wannan shi ne hanyar da Kungiyar Izala ta dauka a cikin dukkan wa'azinta duk kuwa da cewa a mazhabar Malkiyyah halal ne mutum ya daura laya ko gurun da yake dauke da wasu ayoyin Alkur'ani ko kuma wasu kalmomi na ambaton Allah, kamar yadda ya zo cikin littattafan fikhun Malikiyyah kamar haka:- 1. Ya zo cikin Alfawaakihud Dawaanii sharhin Risalah t1/340 kamar haka:- ((ولا باس بالمعاذة وفيها القران)) Ma'ana: ((Babu laifi a daura layar da Alkur'ani yake cikinta)). 2. Ya zo cikin Jawaahirul Ikliil sharhin Mukhtasar 1/21 kamar haka:- ((وحرز بساتر وان لحائض)). Ma'ana: ((Layar da baduku ya rufa ta da fata halal ne a rataya ta, koda kuwa mace ce mai haila)). 3. Ya zo cikin As'halul Madaarik kamar haka:- ((يجوز تعليق التمائم وهي العوذة التي تعلق على المريض والصبيان وفيها القران وذكر الله تعالى اذا خرز عليها جلد ويجوز تعليقها على المريض والصحيح خوفا من المرض والعين)). Ma'ana: ((Yana halatta rataye layu, watau abin tsarin da ake rataya wa mara lafiya da kuma yara, alhali akwai Alkur'ani ko ambaton Allah Madaukaki a cikinsu, matukar dai an rufa layun da fata. Kuma rataya su na halatta ga mara lafiya, da ma wanda yake mai lafiya ne, saboda tsoron kada ya kamu da rashin lafiya ko kambun baka)). Muna rokon Allah da Ya tabbatar da dugaduganmu a kan ingantattun Sunnonin ManzonSa mai tsira da amincin Allah. Ameen. DR IBRAHIM JALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 218 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853