BIDI'A ADDININ RUDU DA SON ZUCIYA:

Dazu a BBC nake jin wani dan bidi'a daga garin Bauci yana kafa hujjar bidi'ar bukin maulidin Inyas da suke yi da Aya ta 114 cikin Suuratun Nahl inda Allah Ke cewa:- ((فكلوا مما رزقكم الله حلالا طيبا واشكروا نعمة الله ان كُنتُم إياه تعبدون)) Ma'ana: ((Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku a matsayin halal mai dadi, ku gode ni'imar Allah in kun kasance masu bauta maSa ne)). Wannan dan bidi'ar ya ce: tunda Allah Ya ce a gode wa ni'imarSa, wannan ya shar'anta musu yin bukin maulidin Tijjani, da kuma yin bukin maulidin Inyas!! 1. Ya kamata a san cewa babu wani malamin Tafsiri cikin Magabata da ya fassara wannan bangare na Aya da cewa yana shar'anta bukin maulidin Tijjani da Inyas, ko bukin maulidin wani dan bidi'a mai kamata da su, ko bukin maulidin wani malami na Sunna cikin Malaman Sunna da aka yi tun Lokacin kafuwar Musulunci ina nufin Sahabbai da Taabi'ai da Wadanda suka bi irin hanyarsu. Ke nan kafa hujja da bangaren wannan a kan halaccin bukin maulidin Tijjani da Inyas domin neman lada wani Zaki ta Malle ne Sannan kuma bidi'a ta bata. 2. Babban Malamin Tafsiri wanda ake masa lakabi da Shugaban masu Tafsiri a zamaninsu Muhammad Bin Jariir Attabarii wanda ya mutu a shekarar Hijira ta 310 watau da mutuwarsa yau shekara 1,126 ke nan, wannan babban malamin Tafsiri ya fassara wannan aya cikin littafin tafsirinsa sananne ya ce: ((يقول تعالى ذكره: فكلوا أيها الناس مما رزقكم الله من بهاءم الانعام التي احلها لكم حلالا طيبا مذكاة غير محرمة عليكم. "واشكروا نعمة الله" يقول: واشكروا الله على نعمه التي انعم بها عليكم في تحليله ما احل لكم من ذلك، وعلى غير ذلك من نعمه "ان كُنتُم إياه تعبدون" يقول: ان كُنتُم تعبدون الله فتطيعونه فيما يأمركم وينهاهم)). Ma'ana: ((Wanda ambatonSa ya daukaka yana cewa: Ya Ku Mutane! Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi na dabbobin Ni'ima wadanda Ya halatta su gare ku a matsayin halaliya mai kyau abin da aka yanka, ba wadanda aka haramta muku ba. "Ku gode wa ni'imar Allah" watau Yana cewa: Ku gode wa Allah a kan ni'imominSa wadanda Ya ni'imta ku da su game da halattarwanSa ga abin da Ya halatta muku daga wannan, da ma wanin wannan daga cikin ni'imominSa. "In kun kasance masu bauta ne gare Shi" watau Yana cewa: in kun kasance masu bauta wa Allah ne masu yin maSa da'a cikin abin da Yake umurtan ku Yake kuma hana ku)). Kun ga a nan babu inda wannan babban Malamin Tafsiri Ya ce wannan Ayar tana nufin halatta yin bukin maulidin wani wanda kake ganin yana da hannu cikin koya maka yadda ake ibadar Allah: Zikirin harshe, ko Zikirin gabbai, ko Zikirin zuciya, saboda neman lada da wannan bukin domin kasancewarsa nuna godiya ga Allah. 3. Da wannan Ayar tana nufin halaccin yin bukin maulidin duk wani wanda ke da hannu cikin shiriyar wasu mutane, to da wadanda za su fi cancanta da a yi musu irin wannan bukin saboda neman lada su ne Shabbai, musamman kamar su Abubakar, da Umar, da Uthman, da Ali, da kuma sauran Shidan da aka yi musu bushara da shiga Aljannah tun daga nan Duniya. 4. Tijjani, da Inyas babu abin da suka kawo a Duniya in banda bidi'ar Dariikar Tijjaniyah, da bidi'ar Faidha cikin bidi'ar Dariikar Tijjaniyah, saboda haka babu abin da ya fi dacewa Musulmi ya rika yi game da abin da ya shafe su illa ya nisanci fadawa cikin bidi'o'insu da fadakar da sauran Al'ummar Musulmi iya iyawarsa domin su ma su nisanci fadawa cikin wadannan bidi'o'i da suka zo da su. Kuna dai ganin irin yadda aka yi ta samu a nan cikin ma Nigeria yadda wasu yan fa'idar Tijjaniyah suka yi ta cewa Inyas shi ne Allahnsu! Iyaazan Billah! Allah Ka tausaya mana Ka raba dukkan Musulmi da wannan mummunar bidi'a ta Dariikar Tijjaniyyah, da kuma fa'idar Dariikar Tijjaniyah. Ameen.

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 135 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853