YA KAMATA A SAKE DUBA IRIN AQIIDUN DA KE CIKIN DARIKUN SUFAYE

{وما اريد ان أخالفكم الى ما أنهاكم عنه ان اريد الا الاصلاح ما استطعت وما توفيقي الا بالله عليه توكلت واليه أنيب}. هود: ٨٨. A bara ne muka yi rubutu a cikin Facebook muna masu jinjina wa sheik Abduljabbar a kan matakin da ya dauka na inkarin munkarin da wasu muridan Darikar Tijjaniyyah suka bayyana a fili ta yadda kowa da kowa ma zai iya fahimtar irin kafircin da yake cikin abin da suka fada. To amma a wancan lokacin ni na ce hakan bai isa ba, saboda ya kamata a ce shi Abduljabbar ya kara matsawa gaba ta yadda zai dubi dukkan aqiidun da aka gina Darikun Sufaye gaba dayansu a kansu, sannan ya yi muqaaranarsu da abin da Shari'ar Musulunci mai haske ta zo da shi. Lalle, na fadi hakan ne saboda irin abin da ni na sani game da wadannan darikun. Misali: Dukkan 'Yan Darikar Tijjaniyyah sun yadda da cewa Sheik Ibrahim Khaulaha Shi Gauthu ne! Abin da kuwa suke nufi da Gauthu shi ne: Mai yin abin da yake so cikin duniyan nan, Wanda kome ke fitowa daga gare shi!! Yana rubuce cikin littattafansu irin magana kamar haka:- فالغوث هو الفرد الوحيد الذي يتصرف في العالم فلا يحدث في هذا الكون من امر الا بعد اذنه. وتحت هذا الغوث بدرجة واحدة الأقطاب الاربعة الذين يمسكون جهات الارض وتحتهم الأوتاد السبعة وهم يمسكون بالأقاليم السبعة وتحتهم الأبدال الأربعون!! Ma'ana: Gauthu shi ne makadaicin nan guda daya wanda yake yin abin da ya ga dama, babu wani lamari da yake faruwa a cikin wannan Duniya sai bayan yardarsa. Sannan a karkashin Gauthu da daraja guda akwai Qudubannan guda hudu wadanda suke rike da bangarorin Duniya. Sannan su ma a karkashinsu akwai Autaadannan guda bakwai wadanda suke rike da yankunannan guda bakwai na Duniya. Sannan su ma a karkashinsu akwai Abdaalannan guda arba'in!!! Ke nan daga wannan maganar ce za mu fahimci cewa lazimin duk wanda ya yadda da cewa Shehu Ibrahami Khaulaha Gauthu ne, to kuwa dole ne ya yadda da cewa shi Shehu Ibrahim Khaulaha shi ne mai yin abin da ya ga dama cikin wannan Duniya tamu, shi ne mai rayawa, shi ne mai kashewa, shi ne Mai azurtawa, shi ne mai tsiyatarwa, shi ne kome, shi ne, shi ne.... Saboda haka wadanda suka zagi Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wannan mako a garin Kano saboda nuna nuna farin cikinsu da samuwar Ibrahim Inyas, da Wadanda suka taru a Bauci saboda shi Inyas a gaskiya babu wani Sabo cikin kwamacalar da suka yi a Kano da Bauci wanda da ma ba Shi ne aka gina Darikar Tijjaniyyah a kansa ba. Tabbas Sufanci guba ne kuma babbar musiba ce ga wannan Al'ummah Muhammadiyyah. Muna fata Malamai Sufaye musamman 'Yan Tijjaniyyah a duk inda suke za su kara tunani sosai, sannan su sa tsoron Allah cikin zuciyarsu, su tuna da cewa ita wannan rayuwa ta Duniya ba komai ba ce, su yi wa kan su kiyamul laili su yi watsi da da wadannan munanan akidu, su komo su yi riko da Musulunci kamar yadda Annabi mai tsira da amincin Allah tare da Sahabbansa suka yi. Allah ya taimake mu. Ameen. DR IBRAHIM JALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 123 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853