HUKUNCIN YI WA MAI MULKI INKARIN ABIN DA YA YI BA TARE DA AN KAMA HANNUNSA AN KEBANTA DA SHI CIKIN SIRRI BA:

Wani dan'uwa ya nemi karin bayani game da hakikanin hukuncin wanda ya yi wa Mai Mulki inkari a kan wani abu da ya yi ba tare da ya kama hannun Mai Mulkin ya kebanta da shi cikin sirri ba; watau Mujtahidi yi wa Mai Mulkin Inkari a bayyane: ko dai a gaban shi Mai Mulkin, kuwa a bayan idon shi? To domin amsa wannan tambayar yana da kyau mu yi bayani kamar haka: Na daya: Mujtahidi watau Malamin da ya cancanci yin umurni ko hani da sunan Shari'ah tana yiwu wa ya yi Ijtihadi ya kai ga matsayin daukar yin inkari a bayyane ba a asirce ba ga Masu Mulki; saboda bayyanar Maslaha cikin yin hakan da kuma rashin aukuwar barna a kan Al'umma cikin yin hakan, kamar yadda da yawa daga cikin manyan Malaman Sahabban Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah suka yi a zamaninsu. Na biyu: littattafan tarihin Musulunci da kuma Hadithan da babu sabani cikin ingancin isnadansu suna nuni a kan rashin haramcin yi wa Mai Mulki inkari a bayyane. Misali hadithi na 6774 cikin Sahihul Bukhariy, da hadithi na 4874 cikin Sahihu Muslim, wanda Sahabi Ubaadah Bin Saamit ya ruwaito ya ce:- ((بايعنا رسول الله صلى الله عليه وسلم على السمع والطاعة في العسر واليسر والمنشط والمكره وعلى أثرة علينا وعلى ان لا ننازع الامر أهله وعلى ان نقول بالحق أينما كنّا لا نخاف في الله لومة لائم)). Ma'ana: ((Mun yi wa Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah mubaya'ah a kan yin sauraro da da'ah cikin wahala da sauki, cikin jin dadi da rashin jin dadi, kuma a kan koda an fififta waninmu a kan mu, kuma a kan kada mu yi ja-in-ja da masu lamarin a kan lamarin, kuma a kan mu rika fadin gaskiya a duk inda muka kasance, ba za mu ji tsoron zargin mai zargi ba game al'amarin Allah)). Wannan yana nuna mana cewa fadar gaskiya a kan masu Mulki watau yin musu inkari ba ya kebantuwa da cewa sai an kebanta da su tukun cikin sirri, a'a mai inkari yana iya yin inkarin a duk inda ya kasance matukar dai gaskiya ne abin da zai fadan, wannan shi ne abin da wannan hadithin yake nuna wa. Na uku: Imam Ibnu Jarir Attabariy ya ruwaito cikin Taarikhut Tabariy 3/7 game da labarin karyar da wani ya kawo wa Nana A'isha kamar haka:- ((عن عبيد الله بن عمرو القرشي قال: خرجت عايشة رضي الله عنها وعثمان محصور، فقدم عليها مكة رجل يقال له اخضر، فقالت ما صنع الناس؟ فقال: قتل عثمان المصريين. قالت: انا لله وانا اليه راجعون أيقتل قوما جاءوا يطلبون الحق وينكرون الظلم؟ والله لا نرضى بهذا)). Ma'ana: ((An karbo daga Ubaidul Lahi Bin Umr Al-qurashiy, ya ce: A'isha Allah Ya kara mata yarda ta yi tafiya alhalin Uthman yana wanda aka yi masa kofar-rago. Sai wani mutum da ake kira Akhdar ya je Makka ya same ta, ta tambaye shi ta ce: Mene ne mutane suka aikata (a Madina)? Sai ya ce: Uthman ya kashe Misrawan. Sai ta ce: Inna Lillahi wa Inna Ilaihi Raaji'un! Yanzu ya kashe mutanen da suka zo suna neman gaskiya kuma suna inkarin zalunci? Wallahi! Ba za mu taba yarda da haka ba)). A nan Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta yi wa Sayyidina Uthman Allah Ya Kara masa yarda inkari a filin Allah sannan kuma a bayan idonsa ba wai a gabansa ba. Na hudu: An samu hadithai ingantattu da yawa wadanda suke tabbatar da irin yadda Manyan Maluman Sahabbai Wadanda suka yi wa masu mulki inkari a bainal jama'a ba wai sai sun kebanta da su a asirce ba. Misali:- 1. Babban Sahabi Ubaadah Bin Saamit wanda ya yi inkari wa Khalifah Mu'awiyah, kamar yadda ya zo cikin Sahihu Muslim hadithi na 1587. 2. Babban Sahabi Abuu Sa'id Al-Khudriy, wanda ya yi inkari wa gwamnan Madinah Marwan Bin Al-hakam, kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhariy hadithi na 956. 3. Sahabi Abuu Shuraih Khuwailid Bin Amr Al-Khuzaa'iy, wanda ya yi inkari wa Amr Bin Sa'id Gwamnan Madina, kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhariy hadithi na 104, da Sahihu Muslim hadithi na 1354. 4. Sahabi Abuu Mas'ud Al-Ansaariy Uqbah Bin Amr, Wanda ya yi inkari wa Gwamnan Iraq Al-Mugiirah Bin Shu'ubah. Kamar yadda Ya zo cikin Sahihul Bukhariy Hadithi na 522' da Sahihu Muslim hadithi na 611. 5. Sahabi A'a'iz Bin Amr Al-Muzaniy, Wanda ya yi inkari wa Ubaidillah Bin Ziyad Gwamnan Basrah kamar yadda ya zo cikin Sahihu Muslim hadithi na 1830. 6. Wani mutum daga cikin Sahabbai -wasu Malamai sun ce shi ne Abuu Mas'ud Al-Ansaariy- wanda ya yi inkari wa Gwamnan Madinah Marwan Bin Al-Hakam, kamar yadda ya zo cikin Sahihu Musulim hadithi na 186. 7. Sahabi Umaarah Bin Ru'aibah wanda ya yi inkari wa Bishr Bin Marwan Gwamnan Kufah, kamar yadda ya zo cikin Sahihu Muslim hadithi na 2053. -Nassin Hadithin farko:- ((عن ابي قلابة قال: كنت بالشام في حلقة فيها مسلم بن يسار فجاء ابو الأشعث. قال: قالوا ابو الاشعث ابو الاشعث. فجلس فقلت له: حدث اخانا فيما غنمنا انية من فضة، فامر معاوية رجلا ان يبيعها في أعطيات الناس فتسارع الناس في ذلك فبلغ عبادة بن الصامت رضي الله عنه، فقام فقال: أني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم ينهى عن بيع الذهب بالذهب والفضة بالفضة والبر بالبر والشعير بالشعير والتمر بالتمر والملح بالملح الا سواء بسواء عينا بعين، فمن زاد او ازداد فقد أربى. فرد الناس ما اخذوا، فبلغ ذلك معاوية فقام خطيبا فقال: الا ما بال رجال يتحدثون عن رسول الله صلى الله عليه وسلم احاديث قد كنّا نشهده ونصحبه فلم نسمعها منه! فقام عبادة بن الصامت فأعاد القصة، ثم قال: لتحدثن بما سمعنا من رسول الله صلى الله عليه وسلم وان كره معاوية او قال وان رغم ما أبالي الا ان لا أصحبه في جنده ليلة سوداء)). Ma'ana: ((Daga Abu Qilaabah, ya ce: Na kasance a Sham cikin wani majalisin ilmi, cikinsa akwai Muslim Bin Yasaar, sai Abul Ash'ath ya zo ya ce: Sai suka ce: Abul Ash'ath Abul Ash'ath, sai ya zauna, sai na ce da shi: Dan'uwanmu gaya mana hadithin Ubadah Bin Saamit, ya ce: to, mun tafi wani yaki alhali Mu'awiyah shi ne jagoran mutane, sai muka sami ganima mai yawa, cikin ganimar da muka samu akwai butar azurfa, sai Mu'awiyah ya umurci wani mutum ya sayar da ita da azurfar da mayaka za su samu na ganima wacce nauyinta ya zarce nauyin butar azurfar, sai mutane suka zaburo domin saye, sai labarin hakan ya riski Abuu Ubaadah Bin Saamit, saboda haka sai ya mike tsaye ya ce: Lalle ni na ji Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana hana sayar da Zinari da Zinari, da Azurfa da Azurfa, da Alkama da Alkama, da Dabino da Dabino, da Gishiri da Gishiri sai in suna daidai da juna kuma cinikin ya zama hanu da hanu, duk wanda ya yi kari ko ya nemi kari to lalle ya yi ci Riba. Sai mutane suka dawo da abin da suka saya. Sai labarin haka ya riski Mu'awiyah, sai ya mike tsaye yana mai huduba ya ce: Me ya sa wasu mutane za su rika ambaton wasu hadithai daga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah alhalin mun kasance muna halartar shi muna kuma zama tare da shi amma ba mu ji su daga gare shi ba? Sai Abuu Ubaadah Bin Saamit ya mike tsaye ya maimaita kisser sannan ya ce: Wallahi za mu rika fadar abin da muka ji daga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ko da Mu'awiyah ba ya son hakan, kuma ba ni da wata damuwa don ban tafi tare da shi ba cikin rundunar shi cikin wani dare mai yawan baki)). Nassin hadithi na biyu:- ((عن ابي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يخرج يوم الفطر والأضحى الى المصلى، فاول شيء يبدأ به الصلاة، ثم ينصرف فيقوم مقابل الناس والناس جلوس على صفوفهم فيعظهم ويوصيهم ويأمرهم فان كان يريد ان يقطع بعثا قطعه او يأمر بشيء امر به ثم ينصرف. قال ابو سعيد: فلم يزل الناس على ذلك حتى خرجت مع مروان وهو أمير المدينة في اضحى او الفطر فلما اتينا المصلى ادا منبر بناه كثير بن الصلت فإذا مروان يريد ان يرقيه قبل ان يصلي، فجبذت بثوبه فجبذني فارتفع فخطب قبل الصلاة، فقلت له: غيرتم والله! فقال: أباً سعيد! قد ذهب ما تعلم. فقلت: ما اعلم والله خير مما لا اعلم. فقال: ان الناس لم يكونوا يجلسون لنا بعد الصلاة فجعلتها قبل الصلاة)). Ma'ana: ((Daga Abu Sa'id Al-Khudriy Allah Ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya kasance yana fita zuwa Masallacin Idi a ranar Karamar Salla da Babbar Salla, farkon abin da yake farawa da shi ne yin salla, sannan kuma sai ya juyo ya tsaya ya fiskanci mutane su kuwa mutane suna zaune cikin sahunsu, sannan ya yi musu wa'azi ya yi musu wasiyya, ya yi musu umurni, in kuma yana son ya ayyana wasu mutane saboda zuwa wani yaki sai ya ayyana su, ko yana son ya yi umurni da wani abu sai ya yi, daga nan sai ya juya. Abu Sa'id ya ce: Mutane ba su gushe a kan haka ba har lokacin da na fita tare Marwan a Idin Layya ko a Idin Azumi a lokacin yana Gwamnan Madina, a lokacin da muka zo Masallacin Idi sai ga wani mimbarin da Katheer Bin Sult ya gina sai ga Marwan yana son ya hau mimbarin tun kafin ya yi salla, saboda haka na kamo rigarsa na fisgo shi kuma ya fisgo ni, daga nan ya hau sama ya yi huduba kafin yin salla. Sai na ce da shi: Wallahi kun jirkita. Sai ya ce: Abin nan da ka sani tuni ya riga ya wuce. Ni kuwa sai na ce: Wallahi abin nan da na sani yi fi abin da ban sanin ba alheri. Sai ya ce: Ai mutane ne ba sa zama bayan salla domin sauraron mu saboda haka ne na maida (hudubar) kafin Salla)). Nassin hadithi na uku:- ((عن ابي شريح العدوي رضي الله عنه انه قال لعمرو بن سعيد وهو يبعث البعوث الى مكة اءذن لي أيها الامير أحدثك قولا قام به رسول الله صلى الله عليه وسلم الغد من يوم الفتح، سمعته أذناي ووعاه قلبي وأبصرته عيناي حين تكلم به: انه حمد الله واثنى عليه ثم قال: ان مكة حرمها الله ولم يحرمها الناس فلا يحل لامرء يؤمن بالله واليوم الاخر ان يسفك بها دما ولا يعضد بها شجرة، فان احد ترخص بقتال رسول الله صلى الله عليه وسلم فيها فقولوا له ان الله إذن لرسوله ولم يأذن لكم وإنما إذن لي ساعة من نهار وقد عادت حرمتها اليوم كحرمتها بالامس وليبلغ الشاهد الغاءب". فقيل لابي شريح: ما قال لك عمرو؟ قال: أنا اعلم بذلك منك يا أبا شريح، ان الحرم لا يعيذ عاصيا ولا فارا بدم ولا فارا بخربة)). Ma'ana: ((Daga Abu Shuraih Al-Adwiy Allah Ya Kara masa yarda cewa ya ce da Amr Bin Sa'id a lokacin da yake tsara rundunonin soja domin tura su yaki Makka: Yi mini izini Ya Gwamna domin in gaya maka wata maganar da Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi a kashe garin Fathu Makka, na ji ta da kunnuwana biyu, da kiyaye ta da zuciyata, na gan ta da idanuna biyu a lokacin da ya hurta ta; Hakika ya gode wa Allah ya kuma yabe Shi sannan ya ce: Lalle Allah ne Ya haramta Makka ba mutane ne ba suka haramta ta, saboda haka ba ya halatta ga mutumin da ya yi imani da Allah da kuma Ranar Lahira ya zubar da jini a cikinta ko ya yanke wata itaciya a cikinta, Idan kuma wani ya ce ai babu kome a yi yaki a cikinta saboda Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi yaki a cikinta to ku ce masa: Allah Ya yi izini ne ga ManzonSa ku kuwa bai yi muku ba, ni ma kuwa Ya yi mini izini ne na wani lokaci guda, daga nan kuma haramcinta ya sake dawowa kamar yadda yake a jiya, duk wanda ya halarci wannan bayani ya isar da shi ga wanda bai halarta ba. To sai aka ce da Abu Shuraih: Mene ne Amr ya gaya maka? Ya ce: Ni na fika sanin wannan Ya Shuraih! Lalle Harami ba ya boye mai sabo, ko wanda ya kashe wani ya gudu, ko wanda ya yi wata barna ya gudu)). Nassin hadithi na hudu:- ((ان عمر بن عبد العزيز اخر الصلاة يوما فدخل عليه عروة بن الزبير فأخبره ان المغيرة بن شعبة اخر الصلاة يوما وهو بالكوفة فدخل عليه ابو مسعود الأنصاري فقال: ما هذا يا مغيرة؟ أليس قد علمت ان جِبْرِيل نزل فصلى فصلى رسول الله صلى الله عليه وسلم ثم صلى فصلى رسول الله صلى الله عليه وسلم ثم صلى فصلى رسول الله صلى الله عليه وسلم ثم صلى فصلى رسول الله صلى الله عليه وسلم ثم صلى فصلى رسول الله صلى الله عليه وسلم. ثم قال: بهذا امرت، فقال عمر لعروة انظر ما تحدث يا عروة او ان جِبْرِيل عليه السلام هو أقام لرسول الله صلى الله عليه وسلم وقت الصلاة؟ فقال عروة كذلك كان بشير بن ابي مسعود يحدث عن ابيه)). Ma'ana: ((Cewa wata rana Umar Bin Abdul Aziz ya jinkirta salla sai Urwah Bin Zubair ya shigo masa ya ba shi labarin cewa Mugiirah Bin Shu'ubah ya jinkirta salla wata rana a garin Kuufah, sai Abul Mas'udul Ansaariy ya shigo masa ya ce: Kai Mugiirah mene ne wannan? Ba ka kasance ba ne kana sane da cewa Jibirilu ya sauko ya yi salla sannan Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi salla? Sannan ya yi salla kuma Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi salla? Sannan ya yi salla kuma Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi salla? Sannan ya yi salla kuma Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya yi salla? Sannan ya yi salla kuma Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi salla? Sannan ya ce da wannan aka umurce ni? Sai Umar ya ce wa Urwah: Kai Urwah ka rika yin nazarin abin da kake fadar shi, yanzu lalle Jibirilu shi ne ya yi wa Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah limanci lokacin salla? Sai Urwah ya ce: Lalle haka nan ne Bashir Bin Abi Mas'ud Ya kasance yana tadawa daga mahaifinsa)). Nassin hadithi na biyar:- ((ان عاءذا بن عمرو وكان من اصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم دخل على عبيد الله بن زياد فقال: اي بني! اني سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: ان شر الرعاء الحطمة، فإياك ان تكون منهم. فقال له: اجلس فانما انت من نخالة اصحاب محمد صلى الله عليه وسلم! فقال: وهل كانت لهم نخالة؟ إنما كانت النخالة بعدهم وفي غيرهم)). Ma'ana: ((Lalle A'a'iz Bin Amr -wanda yake daya ne daga cikin Sahabban Manzon Allah Mai tsira da mincin Allah- ya shigo wajen Ubaidul Lah Bin Ziyad sannan ya ce: Ya Dana! Lalle ni na ji Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah yana cewa: Mafi sharri cikin makiya ya shi ne mabarnacin da ya tausayin dabbobinsa, to ina maka kashedin kada ka zamanto cikinsu. Sai ya ce da shi: Zauna, kai ba kowa ba ne face daga cikin makaskantan Sahabban Muhammad mai tsira da amincin Allah! Sai ya ce: Ashe suna da makaskanta? Gaskiyar lamari shi ne ana samun makaskanta ne bayansu ko cikin wasunsu)). Nassin hadithi na shida:- ((عن ابي بكر بن ابي شيبة قال: اول من بدا بالخطبة يوم العيد قبل الصلاة مروان، فقام رجل فقال: الصلاة قبل الخطبة. فقال: قد ترك ما هنالك. فقال ابو سعيد: اما هذا فقد قضى ما عليه، سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول: من رأى منكم منكرا فليغيره بيده فان لم يستطع فبلسانه فان لم يستطع فبقلبه وذلك اضعف الإيمان)). Ma'ana: ((Daga Abu bakr Bin Shaibah ya ce: Farkon wanda ya fara yin huduba Ranar Idi kafin yin salla shi ne Marwan, sai wani mutum ya tsaya ya ce: Salla kafin yin huduba. Sai ya ce: Tun tuni an bar wannan. Sai Abuu Sa'id (Al-Khudriy) ya ce: Amma shi wannan hakika ya yi abin da yake kansa, na ji Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah yana cewa: Duk wanda ya ga munkari daga cikinku ya jirkita shi da hannunsa, in ba zai iya ba da to ya yi da harshensa, in ba zai iya ba to ya yi da zuciyarsa)). Nassin hadithi na bakwai:- ((عن عمارة بن رويبة قال: رأى بشر بن مروان على المنبر رافعا يديه فقال: قبح الله هاتين اليدين لقد رأيت رسول الله صلى الله عليه وسلم ما يزيد على ان يقول بيده هكذا. وأشار بإصبعه المسبحة)). Ma'ana: ((Daga Umaarah Bin Ru'aibah ya ce: Na ga Bishr Bin Marwan a bisa mimbari yana mai daga hannayensa biyu, sai ya ce: Allah wadaran wadannan hannaye biyu, hakika na ga Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ba ya yin kari a kan ya ce da hannunsa kamar haka. Sai ya yi ishara da yatsarsa manuniya)). ********************** Ke nan wadannan hadithai da ma wasu Hadithan masu kama da su suna koya mana cewa shi yin inkari ga Masu Mulki a bayyane ko a boye wani abu ne da ya kamata Mujtahidi ya dubi irin yanayi, da kuma irin halin da ake ciki, sannan daga nan sai ya yi abin yake ganin shi ne zai fi zama maslaha, da tasiri a kan kawar da wata barna ta Mai Mulki. Lalle abu ne da ba zai da ce ba, a ce za a yi wa wannan mas'alar bugun kadanya; watau a rika cewa har kullum: Sam ba daidai ba ne Mujtahidi ya rika yi wa Mai Mulki inkari bayan ya kebantu da shi cikin sirri ba. Ko kuma a rika cewa: Sam ba daidai ba ne ba Mujtahidi ya rika yi wa Mai Mulki bayyanannar inkari a kan barnar da yake yi ba. Tabbas wannan lamari yana bukatar I'itidali da barin dukkan wani nau'i na ta'assubanci. *********************** WANI HADITHI DA YA ZO CIKIN WANNAN BABI: Imam Ahmad ya ruwaito hadithi na 15369 daga Sahabi Iyadh Bin Ganm wanda yake Magajin Birnin Daaraa ne a Iraq Allah ya kara masa yarda ya ce Manzon Allah Mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((من أراد ان ينصح لسلطان بأمر فلا يبد له علانية ولكن لياخذ بيده فيخلو به فان قبل منه فذاك وإلا كان قد أدى الذي عليه له)). Ma'ana: ((Duk wanda ya yi nufin yi wa wani Mai Mulki nasihar wani al'amari to kada ya bayyana masa a fili, a'a ya rike hannunsa ya kebantu da shi idan ya karba masa to dama haka ake so, in kuma bai karba ba to shi dai ya ba da hakkinsa da ke kan shi)). Akwai ma wasu Malaman da suka ruwaito wannan hadithin banda shi Imam Ahmad, sannan kuma ya zo ta hanyoyi daban daban wadanda ba su wofinta daga rauni ba, to amma dai idan aka hada hanyoyin nasa za a ba shi darajar inganci. A gaskiya idan aka yi nazari mai zurfi za a fahimci cewa shi wannan hadithi ba ya haramta wa Mujtahidai gaba dayansu yi wa Masu Mulki inkari a bayyane; saboda abubuwa kamar haka:- 1. Wannan hadithi mafiya yawan Sahabban Manzon Allah ba su fahimci cewa yana haramta wa dukkan Mujtahidai yi wa Masu Mulki inkarin wata barna tasu a bainar jama'a ba, saboda ingantattun hadithai da muka kawo a sama a inda manyan Sahabban suka yi wa wasu daga cikin Masu Mulki inkari a cikin jama'a, da kuwa sun fahimci wannan haramci da ba su yi ba, musamman ma idan aka fahimci cewa shi inkarin munkari da kuma nasiha ana yin su ne wani lokaci a bayyane wani lokaci kuma a cikin sirri, watau gwargwadon yadda hali ya kama. Saboda abin Allah Ya hikaita mana cikin Suratu Nuhin Aya ta 9:- {ثم اني أعلنت لهم وأسرت لهم اسرارا}. Ma'ana: ((Sannan ni na bayyana musu, kuma na sirranta musu sirrantawa)). 2. Malaman Shari'a sun tafi a kan cewa: Asalin lamari game Hani shi ne ya kawo haramci, sai dai idan aka samu wani dalili da zai kauda shi daga haramci zuwa ga rashin haramci, tabbas kasancewar mafi yawan Sahabbai sun yi inkari wa Masu Mulki a bayyane a fili ba sai da suka kebanta da su ba suka gaya musu, lalle wannan hakika za ta kauda wannan hani da ya zo cikin hadithin daga nuni a kan haramci zuwa ga nuni a kan wani amma ba haramci ba. 3. Ana iya cewa wannan hanin da Ya zo cikin wannan hadithi ya kebanta ne da Mujtahidin da yake da ikon ya zo gurin Mai Mulkin ya kuma iya kama hannunsa sannan ya kebantu da shi shi kadansa, amma Mujtahidin da ba yi da wannan ikon ba yi da wannan damar sai ya koma kan abin da yake shi ne asali; watau ya koma ya yi inkarin da zai yi gwargwadan yadda ya saukaka a gare shi: Ko dai ya yi inkarin cikin majalisinsa ba ilmi, ko kuwa ya yi inkarin a kan mimbarin masallacinsa, ko kuwa ya yi inkarin a duk inda yin wa'azi yake halal ne a gare shi. Muna rokon Allah Ya taimake mu Ya dora mu a kan daidai har kullum. DR IBRAHIM JALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 28 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853