BIDI'AH IN TA BUNKASA CIKIN MAI YIN TA TANA IYA MAIDA SHI MAHAUKACI:

Yanzun nan na saurari abin da wani jahilin dan bidi'ah cikin rigar Malamai daga garin Jos ya ce na karyata gaskiyar da Mahankaltan Nigeria suka sani game da Sunnah TV da Manara TV da Manara Radio, da kuma abin da suka sani game da seminar da Katsina 2015 inda ya yi ta cewa -babu tsoron Allah babu kuma kunyar jama'ar Nigeria su yi masa dariya- dukkan wadannan haqaa'iq, dukkan wadannan tabbatattun lamura karya ce babu su! Ya ce: babu wani abu da ake kira Sunna TV ko Manara TV ko Manara Radio, Sannan babu wani abu da aka yi na Seminar a garin Katsina 2015! Allah wadaran bin hanyar Bidi'ah da da bin hanyar son zuciya. Tabbas da wasu Larabawa ke cewa: "Wal Junuunu Funuunu" hakika sun yi gaskiya cikin abin da suka fada; saboda ga shi ta fito fili cewa shi wannan jahili cikin rigar Malamai na garin Jos shi kuwa irin nau'in haukarsa ke nan. Allah Ya tsare mu da sharrin bidi'ah. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 55 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853