HUKUNCIN YIN ALLURAR RIGA-KAFIN CUTAR POLIO:

Wannan shi ne tarjamar nassin fatawar Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya game da allurar rigakafin cutar Polio. Ita dai wannan fatawa ta Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya an yi ta ne a ran 7/6/1434 H 17/4/2013 M a garin Jiddah a Kasar Saudi Arabia. Ga nassin fatawar: ((Bayani na biyu daga babbar majalisar fiqhun Musulunci ta Duniya game da sha'anin wajibcin yin allurar rigakafin cutar polio: Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga annabinmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa gaba daya. Bayan haka: Lalle majalisar fiqhun Musulunci ta Duniya wacce ta samo asali daga Kungiyar taimakon juna ta Musulunci, lura da ta yi na matsayinta cikin Musulunci, saboda ganin cewa ita marji'i ne na Fiqhu ga al'ummar Musulmi, da kuma irin yadda ta fahimci wajibcin da aka dora wa Malamai masu nasiha, bayan ta karbi rahotanni kan irin yadda aikin yin allurar riga kafi ya yi nasara a kasashen Musulmi game da dakatar da yaduwar ciwon polio a cikinsu, in banda sashin wasu kasashen kamar su: Pakistan, da Nigeria, da Afganistan, wanda kuma hakan ya zo daidai da sabon kamfen din da gwamnatocin wadannan kasashe suke yi, toh ita (wannan majalisa) tana sabunta kiranta ga iyaye maza da mata, da dukkan masu lura da yara kanana cikin dukkan Duniya, tana kiransu da su ba da hadin kai ga wannan kamfe, su kuma gaggauta yi wa 'yayansu maza da mata allurar riga kafin cutar polio, saboda tabbatar muhimmancin cewa wannan allurar na raba su da sharrin kamuwa -cikin falalar Allah da ni'imarsa- da cutar polio wacce har yanzun nan ba ta da magani in har ta kama mutum, wacce kuma take sabbaba nakasa ta dindin ga mara lafiya. (lalle yin wannan allurar) wajibi ne na shari'ar Musulunci, kuma amana ce a wuyayen shugabannin yara, su ne kuma za su dauki zunubin kin yi wa yaransu wannan allurar. Hakika ya tabbata daga bangarorin da suke da hakki a kasashen Musulmi cewa wannan allura babu wani abu a cikinta da yake da alaka da alade, sannan kamar yadda wadanda aka amince da ilminsu suka tabbatar babu wani abu cikin allurar da yake hana haifuwa ga mata cikin kwanukan rayuwarsu masu zuwa. Sannan dukkan kasashen Duniya daga cikinsu har da kasashen Musulmi sun yi ittifaki a kan yi wa yara wannan allura ta rigakafin cutar polio, da kuma cewa babu wata cutarwa da ta tabbata a cikinta. Sannan wannan wajibci da yake kan iyaye da shugabanni yana farawa ne tun ranar da aka haifi yaro kuma zai ci gaba har lokacin da ya kai shekaru shida, tare da bin tsarin jadawali na karban allurar kamar yadda aka tsara, saboda fa'idar riga kafi ta tabbata, tare kuma da maida hankali zuwa ga sauran allurai na riga kafi da ake yi wa yaran kamar na: Tuberculosis, da Diphtheria, da Titanous, da Whooping-cough, da Liver disease, da Measles, lalle alluran rigakafi da wasunsa suna da tasiri cikin wadannan cutuka -bayan falalar Allah da minnarsa- watau wajen kauda annoba, da cutuka masu yaduwa wadanda a da can yan adam suka yi ta fama da su, kamar ciwon agana da makamantansa. Hakika Babbar majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya ta halatta wa masu mulki -ganin cewa su ne wadanda umurninsu ke da alaka da maslaha- ta halatta masu tilasta wa mutane yin alluran rigakafi saboda abin da yake cikin yinsa na hana yaduwar cutuka. Lalle ya zo cikin Sakin layi "b" Article na uku na Matsayar Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya, lamba: 67 (7/5) shekara ta 1412 H wanda ya yi daidai da 1992 M game da sha'anin jinya abin da nassinsa ya ce: ((Yana halatta ga masu mulki su tilasta wa mutane yin jinya a wasu lokuta, kamar jinyar cutuka masu yaduwa cikin jama'a, da karban allurar rigakafi)). Lalle Malaman Babban Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya da dukkan masana Fiqhunta wadanda ke wakiltan kasashensu, dukkansu suna da burin su ga cewa matasan al'ummar Musulmi masu zuwa nan gaba sun kasance suna jin dadin rayuwa da irin baiwar da Allah Mabuwayi Ya ba su kamar yadda ya kamata, kuma su kasance suna cikin cikakken koshin lafiya, lamuransu su kasance har karshe lamura ne masu kyau, saboda duk lokacin da aka ce yara mazansu da matansu suna cikin koshin lafiya, to kuwa lalle ana musu tsammanin makoma kyakkyawa. Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya tana yin wasiyya ga dukkan kasashen Duniya saboda kasancewar yaki da polio lamari ne na nuna wa dan adam jinkai, haka nan kuma tana yi wa kasashen Musulmi da sauran kungiyoyinsu kebabbiyar wasiyya, saboda kasancewar mas'alar yaki da cutar polio mas'ala ce da ta shafi Al'umma, da cewa su yi dukkan abin da za su yi saboda su kauda dukkan abin za iya kawo wa yin allurar rigakafi cikas, su yi dukkan abin da za su iya yi domin kawar da dukkan wasu wahalhalu da za su iya hana yin allurar. Sannan a wannan wuri, Sakatariyar Babbar Majalisar Fighun Musulunci ta Duniya tana yin tir da fatawowin da suka fito daga sashin wadanda sawaaba ta nisance su, fatawowin da suke haramta yin allurar riga kafi, fatawowin da suka dogara a kan wasu bayanai mara kan gado, da kuma wasu tunani na kure, fatawowin da aka fitar ba tare da an yi tunanin irin barnar da za su iya jawo ba na cusa yara cikin wannan mugun ciwo ba tare da sun yi wani laifi ba, illa dai kawai iyayensu ne suka yi aiki da fatawowin wadancan mutane. Babbar Majalisar tana yin wasiyya ga masu hudubar masallatai da limamansu, da Malamai masu wa'azi masu kira zuwa ga Allah Mabuwayi, masu shiryarwa masu karantarwa da su kira jama'a a cikin hudubobinsu cewa su bada hadin kai a nan gaba ga aikin allurar rigakafi, sannan kuma su yi aiki domin yakar wancan fatawa wacce take shazzah (fatawar yan tsiraru da ta saba wa fatawar masu rinjaye) wacce take cewa yin allurar rigakafin cutar polio haramun ne, kuma take ta sanya shakka da balbala cikin mutane ba tare wata hujja ko dalili ba. Sannan Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya tana yin tir da babbar murya da abin da sashin masu laifi suka aikata na kashe wani adadi na ma'aikatan allurar rigakafin cutar polio, da ma wasunsu daga cikin ma'aikatan kiwon lafiya, ba tare da sun yi wani laifi ba, da kuma yin garkuwa da wasunsu saboda neman fansa domin neman biyan wasu bukatu kebabbu ko gamammu, abin da Shari'ar Musulunci da ma sauran shari'u, da dokokin kasashen Duniya suka haramta. Haka nan Babbar Majalisa tana yin tir da yin amfani da aikin polio da wasu masu taimakawa aikin ke yi domin biyan bukatun kansu, ko dai a bayyane ko kuwa a boye ta hanyar leken asiri, abin da ba yi da wata alaka da harkar kiwon lafiya, tana yin tir da haka saboda hakan ya saba wa dokokin Duniya da kuma ayyukan kwarai na jinya. Hakika Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya ta fitar da bayani filla-filla a shekarar 1430 H wanda ya yi daidai da 2009 M domin jan hankulan jama'a saboda yin allurar rigakafin polio, bayanin da ya kunshi hukunce-hukunce da kuma dalilai na Shari'ah wadanda suka bayyanar da wajibcin yin allurar rigakafin cutar polio, sannan a yanzu kuma tana kara karfafa abin da ya zo cikin wancan bayanin wanda ma'anarsa a takaice shi ne:- Wajibi ne a kan mutum ya kare jikinsa da jikin iyalansa, ya kuma tsare lafiyarsu, ya nisantar da su dukkan wani abu da zai cutar da su iya karfinsa, saboda fadar Allah Madaukaki: ((Kada ku jefa hannayenku zuwa ga halaka, ku kyautata, lalle Allah Yana son masu kyautatawa)). Suratul Bakara: 195. Yin abin da zai kare lafiyar jikkuna daga dukkan wani abu da zai sa su cikin hatsari yana daga cikin manyan wajibai cikin Shari'ar Musulunci, sannan Ka'idar hana cuta da cutarwa ita ma ta hana hakan, ka'idar da take asalinta shi ne adithin Annabi daga Dan Abbas ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah Ya ce: ((Babu cuta babu cutarwa)). Imam Ahmad ne ya fidda shi cikin Musnad dinsa, da Hakim cikin Mustadrak, da wasunsu. Musulunci ya dora wa iyaye maza da mata dawainiya mai girma game da sanya tsaro ga 'yayansu maza da mata, da kuma kyautata kiwon dukkan sha'anoninsu, daga cikin hakan akwai: Sha'aninsu na lafiya musamman ma wadanda ba su balaga ba daga cikinsu, akwai hadithai da suka zo da hakan daga cikinsu akwai fadarsa mai tsira da aminci: ((Dukkanku masu kiwo ne kuma wadanda ake tambayarsu kiwon da aka ba su, Shugaba mai kiwo ne kuma wanda ake tambayarsa kiwon da aka ba shi ne, Na miji mai kiwo ne cikin iyalansa kuma wanda ake tambayar abin da aka ba shi kiwo ne, Mace mai kiwo ce cikin gidan mijnta kuma wacce ake tambayar abin da aka ba ta kiwonsa ne)). Buhari da Muslim ne suka fitar da shi. Da kuma fadarsa mai tsira da amincin Allah: ((Ya isan ma mutum a matsayin zunubi a ce ya yi watsi da wanda yake iyali ne gare shi)). Almustadrak. Allah Mabuwayi ya yi wa mutum ni'ima da ya halicce shi cikin mafi kyauwun tsari, Mabuwayi ya ce: ((Hakika mun halicci mutum a bisa mafi kyawun tsari)). Suratut Tiin: 4. Mabuwayi Ya yabi annabinSa Zakariyya a lokacin da ya roke shi kyakkyawan zurriyya, neman kyakkyawan zurriyya yana hadawa da lafiyar jiki, Mabuwayi Ya ce: ((A can ne fa Zakariyya ya roki Ubangijinsa Ya ce: Ya Ubangiji Ka ba ni wata zurriyya mai kyau daga gare ka, lalle kai Mai jin addu'a ne)). A'alu Imran: 38. Sannan Musulunci ya kwadaitar da mutum da ya nemi sabuban karfi da kuma dukkan abin da zai taimake shi, an karbo daga Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda ya ce: Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce: ((Mumini mai karfi ya fi alheri kuma ya fi soyuwa a wurin Allah a kan mumini mai rauni, amma akwai alheri a cikin ko wanne daga cikinsu, ka nuna kwadayin samar da abin da zai amfane ka..)). Muslim ne ya ruwaito shi. Akwai hadithai da suka zo game da jan hankali domin neman jinya da sabuban da suka dace wurin jinyar, daga cikinsu akwai fadarsa mai tsira da amincin Allah: ((Ku yi magani lalle Allah Mabuwayi bai sanya wata cuta ba face sai da ya sanya mata magani, in banda cuta guda' watau tsufa)). Abu Dawud, da Tirmizi, da Ahmad ne suka fidda shi. Ana daukan allurar rigakafin cutar polio a matsayin jinya na kariya daga cutar da ake tsoron aukuwarta kafin ta auku, abin da ake kira da harshen zamani magani irin na kariya, hakika Musulunci ya tabbatar da wannan matsayi, saboda ya zo daga Annabi mai tsira da amincin Allah cewa: ((Wanda ya karya da dabino bakwai daga cikin dabinon Madina, to sihiri ko guba ba zai cutar da shi ba)). Buhari ne ya ruwaito shi. Kamar yadda ya tabbatar da shi har yanzu a cikin ka'idodin da ake bi domin a hana yaduwar cuta mai yaduwa cikin jama'a, an karbo daga Annabi mai tsira da amincin Allah cewa ya ce: ((Idan kun ji labarin aukuwar annoba a wata kasa, to kada ku shige ta, idan kuma annoba ta auku a kasar da kuke cikinta to kada ku fita daga cikinta)). Buhari ne ya ruwaito shi. Musulunci yana kira zuwa ga fa'idanta daga dukkan wani bincike, ko wani ci gaba da aka samu na ilmin kimiyya wanda zai saukake rayuwar mutum a wannan Duniya... Lalle shi ya zo ne domin ya tabbatar da alherin mutane da jin dadinsu Duniya da Lahira, Madaukaki Ya ce: ((Ku tambayi ma'abuta ambato in har ku ba ku sani ba)). Annahl: 43. Mai tsarki Ya ce: ((Ba mu aiko ka ba face a matsayin rahama ga Duniya)). Al-Ambiya: 107. Lalle tunkude cutuka ta hanyar yin allurar rigakafi ba ya karo da yin tawakkali, kamar yadda tunkude yunwa, da kishin ruwa, da zafi, da sanyi, ta hanyar yin kishiyoyinsu ba ya karo da shi tawakkalin, a gaskiya ma hakikanin tawakkali ba ya cika sai an yi riko da sabuba na fili wadanda Allah Madaukaki Ya kafa su domin su rika samar da abin da suke sabbabawa ne bisa kaddara da Shari'ah, saboda haka yana yiwuwa barin yin allurar rigakafi ya zama haram matukar dai hakan zai cutar. Wannan shi ne abin da aka rubuta a takaice. Allah Ya yi dadin tsira da aminci ga shugabanmu Muhammad da iyalansa da sahabbansa da wadanda suka bi shi da kyautayi har zuwa ranar Kiyama. Sakataren Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya Professor Ahmad Khalid Babakr Cikin garin Jidda 7/6/1434 17/4/2013)). Intaha. ************************************* Yan'uwa Musulmi wannan ita ce tarjamar fatawar Babbar Majalisar Fiqhun Musulunci ta Duniya game da allurar rigakafin cutar polio, manufarmu da kawo wannan fatawar shi ne fa'idantar 'yan'uwa Musulmi na wannan kasa tamu Nigeria, saboda su san mene matsayin majoratin Maluman Musulunci na Duniya game da wannan allura ta rigakafin cutar polio. Sannan ina jan hankalin 'yan'uwa da su rika yin taka tsantsan cikin lamuransu, su daina gina lamura a kan aatifah ko son wani kawai, ko kuma kin wani kawai, waji bi ne a rika hankalta game da yadda lamura ke kasancewa har su cutar da mutane, ko kuma yadda suke kasancewa har su amfanar da mutane. Lalle zai zama abin mamaki matuka mutane su ki karban shaidar mafiya yawan likitocin Duniya, sannan kuma su karbi shidar mainoratinsu wacce ta saba wa shaidar mafiya yawan!! Haka nan zai zama abin mamaki matuka mutane su yi watsi da fatawar Majoratin Maluman Musulunci na Duniya, su koma suna yi musu jamhuri da yarfe suna cewa su 'yan kanzagin Yahudawa ne, su mutane ne da kafurai suka ba su kudi domin su cutar da al'ummar Musulmi, sannan kuma wai suna yin dukkan abin nan da suke yi ne saboda dogara da wata fatawa da wasu mainorati suka bayar. Haka nan abin mamaki ne matuka, mutane su karyata gwamnatocin kasashe wadanda babban aikinsu shi ne lura da maslahar jama'arsu cikin fannoni daban daban cikinsu kuwa har da fannin kiwon lafiya, su karyata gwamnatocin su daura yin yaki da su ko dai da baki ko kuwa da alkalami, wasu ma har da makami domin akwai masu kai wa masu aikin allurar rigakafin cutar polio hari da makami su kuma kashe wadanda kwanansu suka kare, saboda kawai dogara da bayanan da wasu daidaiku cikin al'umma suka fada!!! Lalle irin wannan manhaji gairi mahsuubil awaaqib shi ne yake kawo hargitsi cikin Kasa da Al'ummah, kuma su jahilai har kullum irin wannan yanayi suke so, inda nan da nan sai ku ga cewa sun fara fiskantar mutane da fasikantarwa, sai kuma kafirtawa, daga nana sai kuma kawo musu hari bisa hujjar cewa su makiya al'ummar Musulmi ne wadanda suka karbi kudin Yahudawa domin cutar da Al'ummah!!! Lalle mu a wannan Kasa ya kamata mu fi kowa takatsantsan, saboda har yanzu ba mu fita ba tukun daga musibar wadanda suka haramta karatun boko, saboda kawai su a ganinsu karatun boko yana karo da addinin Musulunci yana kuma cutar da Musulmi cikin addininsu, suna da irin shubuhohi nasu da suke ambatawa, amma dai majoratin maluman Musulunci sun san da cewa su 'yan hayaniya ne kawai, kuma wannan lamari nasu babu abin da yake yi face cutar da Musulunci da Musulmi. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya nuna mana gaskiya gaskiya ce ya ba mu ikon aiki da ita ya nuna mana karya karya ce ya ba mu ikon guje mata. Ya kuma raba wannan Al'ummah da sharrin 'yan hayaniya da jahilai cikin rigar malamai. Ameen. DR IBRAHIM JALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 53 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853