SALLAR IDI A RANAR JUMA'A CIKIN LITTAFAN FIKHU:

1. Hanafiyyah da Malikyyah sun tafi a kan cewa: Idan Idi da Juma'ah suka hadu a rana guda, to babu mai na'ibantar wani daga cikinsu, saboda haka Mukallafi sai ya sallaci Idi a matsayin Sunnah, sannan ya sallaci Juma'a a matsayin farilla. 2. Shafi'iyyah kuwa sun tafi a kan cewa ne: Idan Idi da Juma'ah suka hadu a rana guda, to kowa da kowa zai sallaci Idi a matsayin Sunnah ya kuma sallaci Juma'a a matsayin farilla, wadanda kawai aka sawwake musu sallar Juma'a su ne mutanen da ke rayuwa can nesa da gari, wadanda Larabawa ke kira: Ahlul Bawaadiy. 3. Hambaliyyah kuwa sun tafi a kan cewa: Idan Idi da Juma'ah suka hadu a rana guda, to duk wanda ya sami damar halartan sallar Idi to yana da damar kin halartan sallar Juma'ah, amma kuma dole ne ya sallaci Azahar, haka nan in shi ne Limamin Juma'ah to nan ma dole ya yi wa Mutane sallar Juma'ah. 4. Taabi'iy Ataa'u da kuma abin da aka ruwaito daga Abdullahi Bin Zubair, da Aliyyu Bin Abi Taalib sun tafi a kan cewa: Idan Idi da Juma'ah suka hadu a rana guda, to duk wanda ya sallaci Idi ba sai ya sallaci Juma'ah ko Azahar ba, a'a Idin kawai ya isam masa. ******************** Ibnu Rushd Al-Hafeed ya ambaci mazhabobin nan duka in banda mazhabar Hambaliyyah, ga abin da yake cewa cikin Bidaayatul Mujtahid 2/219:- ((واختلفوا اذا اجتمع في يوم واحد عيد وجمعة، هل يجزي العيد عن الجمعة؟ فقال قوم: يجزي العيد عن الجمعة وليس عليه في ذلك اليوم الا العصر فقط. وبه قال عطاء، وروي ذلك عن ابن الزبير وعلي. وقال قوم: هذه رخصة لأهل البوادي الذين يردون الأمصار للعيد والجمعة خاصة، كما روي عن عثمان انه خطب في يوم عيد وجمعة فقال: من أحب من أهل العالية ان ينتظر الجمعة فلينتظر، ومن أحب ان يرجع فليرجع، وروي نحوه عن عمر بن عبد العزيز، وبه قال الشافعى. وقال مالك وأبو حنيفة: اذا اجتمع عيد وجمعة فالمكلف مخاطب بهما جميعا: العيد على انه سنة، والجمعة على انها فرض، ولا ينوب احدهما عن الاخر)). Muna rokon Allah Ya taimake ku, Ya sa mu yi wannan Idi lafiya. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 41 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853