SAMUN MASU WA'AZI CIKIN AL'UMMA SABODA A GYARA WASU KURA-KURAN DA AKE YI BABBAN ALHERI NE GA AL'UMMA:

MUKADDIMA: Lalle a samu wasu mutane cikin wata al'umma suna tashi suna yin wa'azi, suna kiran jama'a da su tsaida Sunnah, su kuma gusar da bidi'ah, su lazimci gaskiya cikin dukkan lamari, sannan su yaki karya cikin dukkan kome, lalle wannan alheri ne babba. Idan wani ya ce: ai irin wannan aiki yana jawowa mai yin shi wahalhalu da yawa: wani lokaci ya kan zama sanadiyyar mutuwarsa, ko dukansa, ko zaginsa, ko cin mutuncinsa, ko rasa wani hakki nasa da ya kamata ya samu, saboda haka abin da ya fi shi ne kowa ya kame bakinsa, domin samun lafiyar jikinsa, da mutuncinsa. To sai a ba shi amsa da cewa: Ai malamai magada suke ga Annabawa, su kuwa Annabawa ba gadon kudi suka bari ba, a'a gadon ilmin sanin gaskiya ne da kuma aiki da gaskiyar ko ana ha-maza-ha-mata. Wannan shi ya sa wasu daga cikinsu suka rasa rayukansu, wasu kuwa aka dudduke su, wasu kuwa aka zazzage su, wasu kuwa aka cicci musu mutunci ta hanyoyi daban daban. Misali: babu irin cin mutuncin da ba a yi wa Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ba, an yayyake shi, an masa raunuka daban-daban, an masa jamhuru an ce shi tababbe ne mahaukaci, an ce mai raba kan jama'a ne, mai kawo hargitsi cikin al'umma... Babban malamin Sunnah masanin Hadithi, da Tafsiri, da Tarihi, da Sirah, Ibnu Katheer ya ce cikin littafinsa Albidayatu wannihayah 3/55-56:- ((عن سعيد بن جبير وعكرمة عن ابن عباس قال: اجتمع علية من اشراف قريش وعدد أسماءهم بعد غروب الشمس عند ظهر الكعبة، فقال بعضهم لبعض: ابعثوا الى محمد فكلموه، وخاصموه حتى تعذروا فيه، فبعثوا اليه ان اشراف قومك قد اجتمعوا لك ليكلموك، فجاءهم رسول الله صلى الله عليه وسلم سريعا، وهو يظن انه قد 'بدا لهم في أمره بدء، وكان حريصا يحب رشدهم ويعز عليه عنتهم، حتى جلس اليهم. فقالوا: يا محمد انا قد بعثنا إليك لنعذر فيك، وانا والله لا نعلم رجلا من العرب ادخل على قومه ما أدخلت على قومك؛ لقد شتمت الآباء وعبت الدين، وسفهت الآلهة وفرقت الجماعة، وما بقي من قبيح الا وقد جئته فيما بيننا وبينك..)). Ma'ana: ((Daga Sa'id Daga Jubair da Ikrimah, daga Dan Abbas ya ce: Shugabannin Quraishawa sun hadu a Dakin Ka'abah, sannan suka aika wa Annabi mai tsira da amincin Allah cewa suna bukatar zama da shi, nan-da-nan Annabi mai tsira da amincin Allah ya je ya same su saboda tsammanin da yake yi na cewa za su musulunta ne, domin yana son musu alheri, kuma ba ya son abin da zai wahalce su. Da ya zo ya zauna a inda suke sai suka ce da shi: Ya Muhammad! Lalle, mun aika Maka ne domin mu yanke uzurinmu gare ka, wallahi mu ba mu taba ganin wani mutum daga cikin Larabawa da ya kawo musiba cikin jama'arsa, kamar yadda ka kawo musiba cikin jama'arka ba. Hakika ka zagi iyayenmu, kuma ka aibanta addininmu, sannan ka maida mahankaltanmu wawaye, ka kuma zagi allolinmu, ka raba kawunan jama'armu. Babu dai wani mummunan abu da ya rage wanda ba ka sanya shi tsakaninmu ba..)). Intaha. Kun ga dai abin mamaki karara a nan, Quraishawa dai kafurai ne masu bautar gumaka, mashaya giya, maciya riba, masu aikata kusan dukkan nau'i na sabo, amma kuma su ne suka sa Annabi a gaba suna zazzaro masa wadannan maganganu!! Suna cewa shi mai raba kawunan jama'a ne saboda kawai ya ce da su su bi Addinin gaskiya, su kuma lazimci gaskiya su daina karya, da hasada, da hikdu, su daina karban umurnin kowa matukar dai ya saba wa umurnin Allah Madaukakin Sarki. Wannan ita ce al'adar karkatattu cikin ko wane zamani, sawa'un kafurai ne masu bautar gumaka, ko kuwa Yahudawa ne da Nasara, ko kuwa cikin jumlar Musulmi ne suke. A lokacin da Sheik Muhammad Dan Abdullwahhab, ya fara yi wa jama'arsa wa'azin su daina ayyuka irin na shirka da bidi'ah, su tuba su yi riko da Alkur'ani da Sunnah, haka da yawa daga cikin masu mulkinsu, da malamansu da jahilansu suka yi caa a kansa, suka cutar da shi cuta mai yawa! A lokacin da Sheik Uthmanu Dan Fodiyo ya fara yi wa jama'ar kasar Hausa wa'azin su bar ayyuka irin na shirka, da bidi'ah, su dawo zuwa ga Alkur'ani da Sunnah, da yawa daga cikin sarakuna da malaman zamaninsa da jahilan da ke tare da su, sun yi ta musguna masa ta hanyoyi daban-daban. A lokacin da Sheik Abubakar Mahmud Gumi ya fara yin wa'azi kan barnar da take gudana a zamaninsa ta bidi'ar sufaye da abin da ya yi kama da haka, ya kuma shiga rubuce-rubuce domin bayyanar da gaskiyar lamari cikin haka, lalle sarakuna, da malamai, da kuma jahilan da ke tare da su sun yi caa a kansa, sun yi kokarin kashe shi ba sau daya ba, ba sau biyu ba, sun yi kokarin bata masa suna ta hanyoyi daban daban. Sheik Isma'ila Idris a shekarunsa na farko cikin kiransa ga mutane zuwa ga Alkur'ani da Sunnah, da bijire wa surkullen sufaye da sauran bidi'o'i da ke baje cikin Al'umma ya sha wahala matuka, a inda sufayen wancan lokacin da jahilan da ke tare da su suka yake shi iya karfinsu. MAI HANKALI ZAI FARA DA GYARAN KANSA NE SANNAN SAI NA KUSA SAI KUMA NA KUSA HAR IYA KARFINSA: A ka'ida mutum mai hankali zai fara gyaran kuransa ne, kafin ya gyara kuren waninsa, watau zai amfanar da kansa kafin ya amfanar da waninsa. Imam Muslim ya ruwai hadithi na 997 daga Jabir cewa:- ((أعتق رجل من بني عذرة عبدا له عن دبر، فبلغ ذلك رسول الله صلى الله عليه وسلم، فقال: الك مال غيره؟ فقال: لا. فقال: من يشتريه مني؟ فاشتراه نعيم بن عبد الله العدوي بثمانمائة درهم، فجاء بها رسول الله صلى الله عليه وسلم فدفعها اليه، ثم قال: ابدا بنفسك فتصدق عليها، فان فضل شيء فلاهلك، فان فضل عن اهلك شيء فلذي قرابتك، فان فضل عن ذي قرابتك شيء، فهكذا وهكذا)). انتهى. Ma'ana: ((Wani mutum daga kabilar Uzrah ya yanta wani bawa nasa yancin da zai fara aiki bayan mutuwarsa, sai labarin hakan ya kai ga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah, sai ya ce: kana da wani dukiyan ne banda shi (wannan bawan)? Sai ya ce: a'a. To sai (Annabi) ya ce: wa zai sayi wannan bawan daga gare ni? Sai Nu'aimu Dan Abdullahi Ba'adawe ya saye shi da Dirhami dari takwas. Sai Manzon Allah ya zo da su ya mika su gare shi, sannan ya ce: Ka fara da kanka tukun ka yi wa kanka sadaka, idan wani abu ya rage, sannan ka ba wa iyalanka, in ka ba wa iyalanka sannan wani abu ya rage, to sai ka ba wa yan'uwanka makusanta, in ka ba wa yan'uwanka makusanta sannan wani abu ya rage, to sai ka ba wa wannan ka ba wa wancan)). Intaha. Sannan Ibnu Abi Shaibah ya ruwaito cikin Musannaf 7/33 cewa Nakha'ii ya kasance yana cewa in za ka yi addu'a to sai ka fara da kanka tukun)). Har yanzu ya ruwaito a wannan shafin cewa: Said Dan Yasaar ya ce: Na zauna gurin Abdullahi Dan Umar, na ambaci wani mutum, sannan na ce: Allah ya yi masa rahama, sai ya bugi kirjina ya ce: Ka fara da kanka tukuna)). Sannan Imam Attayaalisii ya ruwaito cikin Musnad dinsa 4/35 cewa Abdullahi Dan Amru ya ce:- ((فقلت: يا رسول الله وما تقول في الهجرة والجهاد؟ فقال: يا عبد الله! ابدا بنفسك فاغزها، وابدا بنفسك فجاهدها)). انتهى. Ma'ana: ((Sai na ce: Ya Manzon Allah! Me kake cewa game da Hijira da Jihadi? Sai ya ce: Ya Abdllah! Ka fara da kanka tukun ka yaki kanka, ka fara da kanka tukun ka yi jihadin kanka)). Intaha. Wadannan nassosi suna gwada mana cewa: Lalle mutum mai hankali zai fara gyaran kuransa ne kafin ya gyara kuren waninsa, idan a gidanku ana yin kure ba ka yin shuru amma kuma in a gidan wasu ake yi ka yi magana! A'a za ka gyara kuren gidanku sannan kuma ka gyara kuren gidajen wasu gwargwadon hali. Idan kana cikin wani Club, ko wata Kungiya, ko wasu jama'a kuma ka ga wani kure da ake yi a cikinsu, ba ka cewa tunda jama'arka ne ba za ka yaki kuren da ke cikinsu ba, a'a za ka yi musu wa'azi ka yaki wannan kure nasu gwargwadon hali, wannan shi ne Musulunci, saboda haka ne Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi. Ibnul Athiir ya ce cikin littafinsa Usdul Gabah1/10, da Maawardii cikin littafinsa A'alaamun Nubuwwah 1/275, cewa Ibnu Ishaq ya ce:- ((بعثه الله وله أربعون سنة فأقام بمكة ثلاثة عشر سنة وبالمدينة عشرا. وانه كتم أمره ثلاث سنين فكان يدعو مستخفيا الى ان انزل الله تعالى: وأنذر عشيرتك القربين...)). Ma'ana: ((Allah ya aiko shi yana da shekaru arba'in, kuma ya zauna a Makka shekaru goma sha uku, sannan a Madina shekaru goma. Ya boye lamarinsa na shekaru uku, watau ya kasance yana yin da'awah a boye, har dai lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da: "Ka gargadi danginka mafiya kusa..)). Intaha. Sannan Ibnu Kathiir ya ce cikin littafinsa na Sirah 1/457 Aliyyu Dan Abi Talib ya ce:- ((لما نزلت هذه الآية على رسول الله صلى الله عليه وسلم: "وأنذر عشيرتك الأقربين واخفض جناحك لمن اتبعك من المؤمنين" قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: عرفت أني ان بادات بها قومي رأيت منهم ما أكرهه، فصمت. فجاءني جبريل عليه السلام فقال: يا محمد! ان لم تفعل ما أمرك به ربك عذبك بالنار)). انتهى. Ma'ana: ((Lokacin da ayan nan ta sauka ga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah: "Ka yi wa danginka na kusa kusa gargadi, sannan ka sauko da fiffikenka ga wadanda suka bi ka cikin Muminai" Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Na san cewa lalle ni in har na bayyana wa mutanena (sakon da ke gare ni) zan ga abin da ba na son sa daga gare su, saboda haka sai na yi shiru. Sai Jibrilu amincin Allah ya tabbata gare shi ya zo mini ya ce: Ya Muhammad! Idan har ba ka yi abin da Ubangijinka ya umurce ka da shi ba, to kuwa lalle zai azabtar da kai da Wuta)). Intaha. Daga nan Annabi mai tsira da amincin Allah ya hau dutsen Safaa ya kira dangoginsa na kud-da-kud ya bayyana musu manzancinsa, ya bayyana musu cewa ba zai iya yi wa kowa komi ba a gaban Allah matukar dai bai tsarkake ibada ga Allah Madaukakin Sarki ba. A nan ne da yawa daga cikinsu suka zazzage shi!! A zamanin Annabi na Dawud a wani gari a gabar Matsakaicin farin Teku (Mediterranean Sea) Isra'ilawan garin sun kasu kashi uku: Kashi daya suka saba dokar Allah da ke cikin Attaura wacce ta haramta wa Isra'ilawa yin aiki ranar asabar, suka yi ya yin su a ranar asabar. Kashi na biyu sai suka yi ta yiwa masu wannan su wa'azi suna ce masu abin da suke yi ba daidai ba ne. Kashi na uku kuwa ba su hana masu yin su wannan danyen aiki nasu ba, amma sun ce wa masu yin wa'azin: tunda dai wadannan sun ki karban wa'azi sun ki daina wannan mugun aiki nasu, don me kuke bata lokaci a kan yi wa wadanda Allah zai azabtar wa'azi? To amma da Allah ya tashi yin hukunci sai ya kubutar da masu yin wa'azi, sannan ya azabtar da masu sabon, su kuwa wadanda suka kasa wa'azi, kuma suka yi kokarin gamsar da masu yin wa'azin da su daina, saboda wadanda ake musu wa'azin sun ki ba, Allah bai ba mu labarin abin da ya yi da su ba. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 37 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853