SHAMFI A MAHANGAR SHARI'AR MUSULUNCI

Dazu wani dan'uwa mai suna: Abber Sham'oon ya yi tambaya ta inbox game da hukuncin shamfi a Musulunci. Domin amsa wannan tambayar yana da kyau mu san abubuwa kamar haka:- Na daya: Hadithai sun inganta a kan cewa babu wani tasiri ga shamfi. Imamut Tahaawiy ya ruwaito hadithi na 662 cikin Mushkilul A'athar daga Sahabi Jabir cewa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((لا غول، ولا طيرة، ولا شوم)). Ma'ana: ((Babu (tasirin)wata fataluwa da ake cewa tana cikin daji domin cutar da mutane, babu (tasirin) shamfi da tsuntsaye (wadanda in wani mutum yana son ya yi abu sai ya je ya tada tsuntsaye in sun yi ta hanunsa na dama sai ya yi farin ciki ya yi abin da yake son yi, in kuma sun tashi sun yi ta hanunsa na hagu sai ya yi bakin ciki ya fasa yin abin da yake son yi), babu kuma (tasirin) shamfi (wanda ba irin na tsuntsaye ba)). Sannan Imamul Bukhariy ya ruwaito cikin sahihinsa hadithi na 5380 daga Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((لا عدوى، ولا طيرة، ولا هامة، ولا صفر)). Ma'ana: ((Babu (tasirin) wata rabar cuta, babu (tasirin) shamfi da tsuntsaye, babu (tasirin) wata dabba da ake cewa tana fita daga cikin kayin mutum da wani ya kashe har sai ta kashe shi shi ma, babu (tasirin) shiga bala'i saboda shigowar watan Safar)). Na biyu: Hadithai sun inganta a kan umurni da nisantar gurin da annoba take. Imamu Muslim ya ruwaito cikin sahihinsa hadithi na 2221 daga Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((لا يورد ممرض على مصح)). Ma'ana: ((Kada mutumin da yake da rakuma masu ciwo ya sako su cikin rakuman mutumin da rakumansa lafiyayyu ne)). Imamul Bukhariy ya ruwaito cikin sahihinsa hadithi na 5380 daga Abu Hurairah Allah Ya kara masa yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((فر من المجذوم كما تفر من الاسد)). Ma'ana: ((Ka guje wa mai kuturtan (da yake iya raba) kamar yadda kake guje wa Zaki)). Na uku: Hadithai sun inganta a kan cewa tasirin shu'umci na iya tabbata cikin abu uku. Imamul Bukhariy ya ruwaito cikin sahihinsa hadithi na 2703 daga Abdullahi Dan Umar Allah Ya kara masa yarda cewa manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- ((انما الشوم في ثلاثة في الفرس والمراة والدار)). Ma'ana: ((tasirin shu'umci na iya tabbata cikin abu uku: doki, da mace, da gida)). A wata riwayar:((In har tasirin shu'umci na faruwa to yana faruwa ne game da gida, da matar (aure) da dokin (hawa)). Wani sashin Malamai ya ce: in aka dubi wadannan nau'uka uku na hadithai za a fahimci al'amura kamar haka:- 1. Abin da wata cuta ba ta aukuwa ta hanyarsa, babu kuma wata gamammiyar al'ada ko kebabbiya da ta tabbatar da faruwarta, wannan Shari'ah ba ta daukar sa a bakin kome, kuma tana inkarin sa, wannan kuwa shi ne irin shamfin nan na in tsuntsaye sun yi dama to akwai sa'a, in kuma sun yi hagu to babu sa'a. 2. Abin da aka tabbatar da cewa cuta tana aukuwa ta hanyar shi, kamar irin annoban nan da ake gani, to lalle wannan Shari'a tana amincewa da shi, tana kuma yi wa mutane gargadi a kan shi. 3. Abin da cutarsa ke iya faruwa da wasu mutane, amma ba ya faruwa da wasu mutanen, kamar shu'umcin da mutum ke iya samu daga wurin matarsa, ko daga wurin mijinta, ko daga gidan da yake zama cikinsa, ko daga tabbar da yake hawa, ko daga kayan yakin da yake amfani da shi, to irin wannan nau'i Shari'ah ta halatta wa mutane su yi la'akari da shi. Watau shu'umci irin wannan halal ne in ka gan shi to ka guje masa. Muna rokon Allah Ya taimake mu. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 39 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853