KADA 'YAN MAJALISUNMU SU UMURCI KOWA DA DUKAWA DOMIN GIRMAMAWA:

Wajibi ne 'yan majalisinmu su yi watsi da al'adar umurtan wasu mutane da yin sujuda (dukawa) domin girmama 'yan Majalisa, ko domin girmama ita kanta Majalisar. Sujuda (ko ma wace irin sujuda: sunkuyar da kai ne, ko sunkuyar da baya ne, ko sanya goshi a kasa ne, ko wani abu mai kama da haka ne) ba a yin ta a matsayin gaida wani, ko a matsayin girmama wani. Kafin zuwan Musulunci akwai zamunnan da Allah Ya halatta wa mutane yi wa junansu sujuda saboda gaisuwa da girmamawa. Haka nan kafin zuwan Musulunci akwai zamunnan da Allah Ya halatta wa mutane rikon mutum-mutumi na mutane ko na dabbobi a matsayin abin da ake yi wa garuruwa ko gidaje ado, to amma bayan zuwan Musulunci Allah Ya hana hakan Ya maida shi haramun a bisa doka. Allah na haramta abin da yake so a kan al'ummar da yake so a kuma zamanin da yake so, Yana kuma halatta abin da yake a kan al'ummar da yake so a kuma zamanin da yake so, wannan kuwa shi ne dama ma'anar wani babban bangare na abin da ake kira Ibada. Babu mai kalubalantar Allah a kan cewa don me Ya halatta kaza a zamani kaza sannan kuma Ya haramta shi a zamani kaza!! Muna jan hankalin masu daraja 'yan majalisunmu da su tausaya wa Nigeria da talakawanta su guji yin dukkan wani abu da yin sa bai zama dole ba cikin kyautata zamantakewarmu ta 'yan Nigeria, kamar irin wannan umurni da suke bayarwa na a rusuna domin girmama su ko domin girmama majalisarsu, alhalin akwai sabon Allah mai yawan gaske a cikinsa. Muna kiran masu daraja 'yan majalisunmu da kowanne daga cikinsu ya yi iya iyawarsa domin hana abin da zai kara kawo mana hushin Allah cikin wannan Kasa tamu. Allah Madaukakin Sarki Ya taimake mu. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 38 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853