TA'ADDANCI BA SHI DA WANI KEBABBEN JINSI, KO ADDINI, KO NATIONALITY:

A dai gurin masu hankali na duniya yan hayaniya ba shi aikin ta'addanci ba shi da wani kebabben jinsi, ko kebabben addini, ko kebabben nationality, a'a ana iya samun shi cikin ko wace al'umma, kuma cikin ko wane gungu na mabiya wani addini. Wannan shi ne abin da dukkan mahankalta suka yi ittifaaqi a kan shi. Ke nan babu wani mamaki a samu yan ta'adda cikin masu lkirarin bin addinin Musulunci, ko masu ikirarin bin addinin Kirista, ko masu ikirarin bin addinin Shi'ah, ko masu ikirarin bin addinin yahudu, ko masu ikirarin bin addinin Hindu, ko masu likirarin bin addinin Budda, ko masu ikirarin bin addinin Musulunci, babu wani abin mamaki cikin faruwar haka adai gurin masu hankali. To amma idan a yanzu a wannan zamanin ko wannan Kasar an samu wasu daga cikin jahilan mabiya addinin Shi'ah da suke ikirarin cewa ba a samun yan ta'adda cikin mabiya addinin shi'ah, sai mahankalta su tunatar da su cewa akwai kungiyar da ake kira Mujahidi Khal kungiyar da dukkan membobinta yan kasar Iran ne mabiya addinin Shi'ah Ithnaa Ishriyyah kungiyar da ake kiranta da harshen farisanci da:- سازمان مجاهدين خلق ايران Kungiyar da aka kafa ta tun shekarar miladiyya ta 1965, kuma dukkan gwamnatocin kasar Iran suna membobinta da cewa su yan ta'adda ne tun daga wancan Lokaci har zuwa yau din nan da muke maga. Allah Ka raba mu da sharrin jahilci da kuma sharrin abin da jahilci ke haifarwa. Ameen. HIKAAYAR DA TA ZO CIKIN ALBIDAAYATU WAN NIHAAYAH BA TA DA ISNADI: Hikayar da ta zo cikin littafin Al-Bidaayatu Wan Nihaayah 7/255 na Ibnu Katheer na cewa: "Wasu Sahabbai da wasu Taabi'ai sun yi zaman juyayi a kan kisan Khaliifah Uthman Allah Ya kara masa yarda har na tsawon shekara guda, sannan Sahabi Mu'awiyah Allah Ya kara masa yarda ya rataye rigar Uthman wacce take cike da jini a kan mimbari mutane suna ta kuka a kusa da rigar har na tsawon shekara guda, sannan mafi yawan mazaje sun kaurace wa matansu na tsawon shekara guda saboda nuna juyayin mutuwar Khaliifah Uthman Allah Ya kara masa yarda"!! Wannan magana hikaya ce kawai mara isnadi, hikayar da mataninta ke saba wa zahirin a bin da sahihiyar sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah take koya wa dukkan al'ummar Musulmi a bisa dalilai kamar haka:- 1. Annabi mai tsira da amincin Allah ya riga ya koya wa al'ummarsa abin da za su rika yi a duk lokacin da suka fada cikin wata musiba, musamman ta rashin mani masoyi a gare su, ko rashin wani wanda yake abin girmamawa ne matuka a gare su. Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 3121, da Tirmiziy hadithi na 3511, da Nasaa'iy hadithi na 10,909, da Ahmad hadithi na 16,387, da sanadi sahihi, daga uwar Muminai Ummu Salamah Allah Ya kara mata yarda ta ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- اذا اصابت احدكم مصيبة فليقل انا لله وانا اليه راجعون. اللهم عندك احتسب مصيبتي فاجرني فيها وابدل لي خيرا منها Ma'ana: ((Idan wata musiba ta sami dayanku, to ya ce: lalle mu mallakan Allah ne, kuma mu masu komowa ne zuwa gare Shi. Ya Allah a gurinka ne nake neman samun lada a kan musibata. Ka ba ni lada cikinta. Ka kuma musanya mini da abin da ya fi ta alheri)). Wannan shi ne abin da Annabi ya ce mu rika fada, ba wai mu rika yin kururuwa da la'antar Sahabbai da 'yanyansu ba, ko kuma yin wani abu mai kama da haka cikin ma'ana ba. 2. Imamut Tabaraaniy ya ruwaito cikin Al-Mu'ujamul Kabeer hadithi na 6718, kuma Albaaniy ya inganta shi cikin Silsilatus Sahihah 1106, daga Sahabi Saabit Allah Ya kara masa yarda ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:- اذا اصيب احدكم بمصيبة فليذكر مصيبته بي فانها اعظم المصايب Ma'ana: ((Idan wata musiba ta fada wa dayanku, to ya tuna da irin musibar da ta fada masa saboda rasa n, tabbas lalle ita ce mafi girman dukkan musibu)). Cikin wannan hadithin akwai abubuwa guda biyu muhimmai, na daya: umurnin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi wa al'ummarsa na cewa a duk lokacin da wata musiba ta same su to su tuna da cewa musibar da ta same su a dalilin rasa shi Annabi ta fi ta girma nesa ba kusa ba. Na biyu: kwantar wa al'ummarsa hankali; saboda a duk lokacin da wata musiba ta same su to da sun tuna cewa ai akwai wata babbar musiba da ta dara wannan ma ta taba samun su, watau ita ce musibar rasa rayuwar Annabinsu da suka yi, sai hakan ya sanya nitsuwa a cikin zukatansu. Ba kamar yadda masu addinin la'antar sahabbai suke yi ba, a inda suke juyayin mutuwar Husaini Allah ya kara masa yerda amma kuka ba sa nuna juyayin mutuwar fiyayyen halitta Annabi mai tsira da amincin Allah. 3. Annabi mai tsira da amincin Allah ya haramta kururuwa saboda nuna juyayi a kan mutuwar wani, ko marin kumatu da yayyaga tufafi saboda nuna juyayi a kan mutuwar wani, -me kuke tsammanin mutanen da suke yayyanka jikkunansu da wukake da takubba, ko suke hana wa kawunansu jima'i da iyalansu har na tsawon shekara guda, ko su yi ta yin tattaki a kan manyan hanyoyi sanye da bakaken tufafi maza da mata domin nuna juyayi a kan mutuwar wani-? Imamul Bukhariy ya ruwaito hadithi na 1294 cikin Sahihinsa daga Sahabi Abdullahi Bin Mas'ud Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Aloah ya ce:- ليس منا من لطم الخدود وشق الجيوب ودعا بدعوى الجاهلية Ma'ana: ((Ba ya daga cikinmu, mutumin nan da ya mari kumatu sannan ya kaykkyace tufafi, kuma ya yi kira irin kira na jahiliyya)). Sannan Imamu Muslim ya ruwaito hadithi na 934 cikin sahihinsa daga Sahabi Abu Malik Allah Ya kara masa yarda cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:- اربع في امتي من امر الجاهلية لا يتركونهن: الفخر في الاحساب والطعن في الانساب والاستسقاء بالنجوم والنياحة. وقال: النايحة اذا لم تتب قبل موتها تقام يوم القيامة وعليها سربال من قطران ودرع من جرب Ma'ana: ((Akwai abu hudu cikin al'ummata na al'amarin jahiliyya da ba za su bar yin su ba: alfahari da asali, da sukar asalin wani, da ganin tasirin taurari game da saukan ruwan sama, da kuma yin kururuwa a lokacin mutuwa. Ya ce: mai yin kururuwa saboda mutuwa idan har ba ta tuba ba kafin mutuwarta to za a tsaida ita a ranar Kiyamah tana sanye da tufar narkakken dalma da wata irin rigar kazuwa)). ******************** Lalle da wadannan takaitattun bayanai ne masu hankali za su fahimci cewa: hikayar da ta zo cikin Albidaayah ba ta isnadi ballantana a gina wani hukunci na Shari'ah a kanta. Haka nan za a fahimci cewa shari'ar Musulunci ba ta yi umurni da a riga yawo da rigar mamaci wacce take cike da jini saboda a nuna juyayi a kan mutuwarsa ba. Haka nan ba ta yi umurni da a rataye rigar mamaci wacce take cike da jini a kan mimbari ba saboda a nuna juyayi a kan mutuwarsa. Haka nan Shari'ah ba ta yi umurni da cewa mazaje su nisanci yin jima'i da matansu na tsawon shekara guda ba saboda nuna juyayi a kan mutuwar wani mai mutuwa ba. Hakna nan shari'ar Musulunci ba ta yi umurni da cewa maza da mata su sanya bakaken tufafi su hadu suna ta bin titi-titi da tutoci a hannayensu, da wukake da takubba a hannayensu suna ta yayyanka jikkunansu, suna ta la'antar mafi yawan Sahabbai da 'yayansu saboda su nuna juyayi a kan mutuwar wani ba. Tabbas babu irin wannan umurni cikin littafin Allah mai girma, babu kuma irinsa cikin ingantattun hadithan manzon Allah mai tsira da amincin Allah. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya raba mu da sharrin masu gina addininsu a kan tatsunoni mara isnadi, da daukar la'antar sahabban manzon Allah mai tsira da amincin Allah a matsayin babban jigo cikin addininsu. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 37 · November 22, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853