BA A LULLUBE ZANCE KO RUFIN ASIRI GAME DA LAIFUKAN MUTANEN DA HAKKIN YIN DAIDAI CIKIN AL'UMMA YAKE WUYANSU:

Mutanen da hakkin tabbatar da yin daidai yake wuyansu cikin Al'umma, kamar Alkalai, ko Masu wa'azi idan har suka yi zalunci, ko suka yi ha'inci cikin ayyukansu, suka ci amanar al'ummarsu, toh lalle hukuncinsu shi ne: a kunyata su ta hanyar yayata labarinsu cikin Duniya, sannan a raba su da mukamansu, kuma ba za a sake ba su wani mukami ba koda kuwa sun tuba ne daga baya sun kuma kyautata halayensu. Babban Malami cikin Mazhabar Malikiyyah Burhaanud Diin Ibrahim Bin Farhuun ya ce cikin mash'huurin littafinsa mai suna Tabsiratul Hukkam 2/231:- {انه يجب على القاضي اذا اقر بالجور او ثبت عليه بالبينة العقوبة الموجعة، ويعزل، ويشهر، ويفضح، ولا تجوز ولايته ابدا، ولا شهادته، وان احدث توبة، وصلحت حاله؛ بما اجترم في حكم الله تعالى}. Ma'ana: ((Lalle yana wajaba a kan Alkali idan ya tabbatar da bakinsa cewa ya yi zalunci, ko kuwa hakan ya tabbata a kan shi ta hanyar shaida, wajibi ne a yi masa ukuba mai tsanani, kuma a kore shi daga aiki, sannan a yayata labarin shi, a kuma kunyata shi, daga nan ba ya halatta har abada a ba shi wani mukami, kuma shaidarsa ba ta halatta koda kuwa ya tuba ne halinsa ya kyautata; saboda irin laifin da ya yi cikin hukuncin Allah)). Intaha. ******************************* Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 36 · November 23, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853