SALLAR QIYAAMULLAILI A GOMAN KARSHE NA RAMADAN:

'Yan'uwa Musulmi! Idan muka ce: Qiyaamullaili a goman karshe na watan Ramadan toh muna nufin abin da ake kira: Sallar Taraawiihi ne da kuma sallar Ta'aqiibi gaba daya. ********************************** TAMBAYA: Mene ne ya fi falala ta fiskar Shari'ah? Yin qiyaamullaili cikin masallatai a cikin jama'ah ne, ko kuwa yin sa mutum shi kadai a cikin dakinsa? Farko dai, 'Yan'uwa Musulmi! Ya kamata a san cewa: Malaman Musulunci sun yi ittifaki a kan cewa ita sallar Qiyaamullaili cikin watan Ramadan ya halatta mutane su yi ta cikin jama'ah cikin masallatai, kuma ya halatta kowa ya yi ta shi kadai a cikin dakinsa. Toh amma su Malaman sun yi sabani game da cewa: A ina ne ya fi falalar a yi ta? Cikin jama'ah ne ya fi falala, ko kuwa mutum ya yi ta a dakinsa shi kadansa? Akwai mazhabobi biyu shararru, wadannan kuwa su ne:- (1) Hanafiyyah, da Hambaliyyah, da Shafi'iyyah cikin sahihin kauli a wurinsu, duk wadannan Malaman sun tafi a kan cewa: Sallar Taraawiihi a cikin masallaci cikin jama'ah shi ne ya fi falala a wurin Allah a kan mutum ya yi sallar cikin dakinsa shi kadansa. (2) Malikiyyah kuwa sun tafi ne a kan cewa: Abin da ya fi falala shi ne kowa ya yi sallar Taraawiihinsa da sauran nafilfilin darensa shi kadai a cikin dakinsa. REFERENCES: a- Daga cikin littattafan Hanafiyyah sai a dubi: Al-Mabsuut 2/144, da Bada'i'us Sana'i 1/288, da Al-Fataawal Hindiyyah1/116, da Al-Inaayah 2/236, da Haashiyatu Raddil Muhtar2/47. b- Daga cikin littattafan Shafi'iyyah sai a dubi: Al-Majmuu 4/31,35, da Sharhun Nawawii Alaa Sahihi Muslim 6/39, da Asnal Mataalib1/201. c- Daga cikin littattafan Hambaliyyah sai a dubi: Al-Mugnii1/833, da Al-Furuu1/377. ************************ d-Daga cikin littattafan Malkiyyah sai a dubi: At-Tamhiid 8/116, da Ash- Sharhul zkabiir na Ad- Dirdiir1/315, da Hashiyatul Adwii Alaa Kifaayatut Taalibir Rabaanii 3/438. HUJJOJIN WADANNAN MAZHABOBI GUDA BIYU: Jumhuur sun kafa hujja ne da abu biyu:- Na farko: Hadithin Sahabi Abuu Zarr Allah Ya kara masa yarda ya ce :- ((صُمْنَا مَعَ رَسولِ الله صلى الله عليه وسلم فَلَمْ يُصَلِّ بِنَا حتى بَقِيَ سَبْعٌ مِنَ الشَّهْرِ فقامَ بِنَا حتَى ذَهَبَ ثُلُثُ اللَّيْلِ ثُمَّ لَمْ يَقُمْ بِنَا في السَّادِسَةِ وقَامَ بِنَا في الخَامِسَةِ حتَّى ذَهَبَ شَطْرُ اللَّيْلِ، فَقُلْنَا له يا رسولَ الله لو نفَّلْتَنَا بَقِيَّةَ لَيْلَتِنَا هَذِهِ؟ فَقَالَ إنَّهُ مَنْ قَامَ مَعَ الإمَامِ حَتَّى يَنْصَرِفَ كُتِبَ لَهُ قِيَامُ لَيْلَةٍ. ثُمَّ لَمْ يُصَلِّ بِنَا حَتى بَقِيَ ثَلاَثٌ مِنَ الشهْرِ وصَلَّى بِنَا في الثَّالِثَةِ جمع أَهْلَهُ ونِسَاءَهُ والناس فَقَامَ بِنَا حَتَّى خشينا ان يفوتنا الفَلاَحَ)). Ma'ana: ((Mun yi azumi tare da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah bai yi salla (na nafilan dare) tare da mu ba sai da kwana bakwai kadai suka rage daga watan (Ramadhan) sai ya yi mana limanci (cikin sallar nafilan dare) har ( tsawon) kashi daya cikin uku na dare ya tafi, sannan bai yi mana salla ba a dare na shidan, sai kuma ya yi mana salla a dare na biyar sai da rabin dare ya tafi, sai muka ce: Ya Manzon Allah! Da ka ci gaba da yi mana limancin nafilarmu cikin abin da ya rage na wannan dare namu? Sai ya ce: lalle yadda lamarin yake duk wanda ya yi salla tare da liman har (shi liman) ya gama ya tafi, toh za a rubuta masa ladan sallatar daransa, daga nan bai sake yi mana salla ba sai da kwana uku ya rage daga watar, sai ya yi mana salla a dare na ukun, ya kuma tara iyalansa da matansa da kuma mutane, ya yi mana limanci har muka ji tsoron kada suhur ya kubuce mana)). Intaha. Wannan hadthin Albaanii da sauran malaman hadithi sun inganta shi. Ga kuma wadanda suka ruwaito shi:- Abuu Dawud: 1,377, Tirmizii: 806, Nasaa'i: 1,364, da Ibnu Maajah:4,327, da Ahmad: 21,447, da Ibnu Khuzaimah: 2,206, da Al-Bazzar: 4,042, da Abdurrazzaq: 7,706. Na biyu: Suka ce: Yin sallar Taraawiihi cikin masallatai cikin jama'ah shi ne abin da Umar Dan Khattab da sauran Shabbai suka yi, sannan hakan ya ci gaba cikin al'ummar Musulmi har yau s matsayin wata alama bayyananniya cikin Musulunci, ke nan za a kiyasta wannan salla a kan sallar Idi. ******************************* Su kuwa Malikiyyah sun kafa hujja ne da hadithi na 731 wanda Imamul Bukhari ya ruwaito, da hadithi na 781 wanda Imamu Muslim ya ruwaito daga Sahabi Zaidu Dan Thaabit cewa :- ((ان رسول الله صلى الله عليه وسلم اتخذ حجرة قال: حسبت انه قال: من حصير في رمضان فصلى فيها ليالي فصلى بصلاته ناس من اصحابه، فلما علم بهم جعل يقعد فخرج اليهم فقال: قد عرفت الذي رايت من صنيعكم، فصلوا ايها الناس في بيوتكم فان افضل الصلاة صلاة المرء في بيته الا المكتوبة)). Ma'ana: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi wani dan daki (mai riwaya ya ce) ina tsammani irin na tabarmi a cikin watan Ramadan ya yi ta yin salla a cikinsa na wasu dararai, sannan wasu mutane daga cikin Sahabbai suka yi salla da sallarsa, lokacin da ya fahimci suna bin shi salla sai ya rika zama, sannan ya fito zuwa gare su ya ce: Hakika na san abin nan da na gani na halinku, Ya ku mutane! Ku yi salla cikin gidajenku, lalle sallar da tafi falala ita ce sallar da mutum ya yi cikin gidansa in ba sallar falilla ba)). Intaha. Malaman Malikiyyah suka ce: Wannan nassi ne a kan cewa in ba sallar farilla ba, toh ko wace salla ma yin ta cikin gida shi ne ya fi falala. MAGANAR DA MU MUKA RINJAYAR CIKIN WANNAN MAS'ALA 'Yan'uwa Musulmi! Wadannan maganganu biyu da kuka ji su ne mash'hurai daga cikin maganganun Malaman Musulunci cikin wannan mas'alah, toh amma mu abin da muke ganin cewa nassoshin Shari'ah suna karfafawa cikin wannan mas'alar shi ne cewa: Sallolin Qiyaamullaili, watau: Taraawiihinsu da Ta'aqiibinsu cikin daren goman karshe na Ramadan, toh su wadannan sallolin lalle yin su cikin Masallatai kuma cikin jama'ah shi ne ya fi falala a idanun Shari'ah, a kan daidaiku su sallace su cikin gidajensu, dalili kuwa shi ne: shi hadithin Abuu Zarr, a inda aka ce a cikinsa: "Annabi mai tsira da amincin Allah yana tattaro iyalansa da matansa da kuma sauran mutane sannan ya yi musu limanci cikin sallolin har can kusan asuba suke gamawa". Tunda dai Annabi mai tsira da aminci Allah yana umurtan 'ya'yansa mata, da kuma matansa da sauran mutane yana tara su a masallacinsa domin ya yi musu limancin wadannan salloli cikin wasu kwanakin goman karshe na Ramadan, lalle hakan ya tabbatar mana da cewa: yin hakan shi ne ya fi falala a idanun Shari'ah, saboda shi Annabi mai tsira da amincin Allah ba ya shagaltuwa sai da abin da ya fi falala a idanun Shari'ah. Babban Malami Ibnu Qudaamah ya ce cikin littafin Al-Mugnii 7/334: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ba zai shagaltu ba shi da Shabbansa sai da abin da ya fi falala)). Intaha. Sannan Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa26/54: ((Annabi mai tsira da amincin Allah ba zai ciro (Sahabbansa) daga abu mai falala zuwa ga abin da aka fi shi falala ba, a'a abin da ska sani shi ne: Yana umurtan su ne da abin da yake shi be mafi falala a gare su)). Intaha. Ke nan umumin da ya zo cikin hadithin Zaidu Dan Thaabit na cewa: ((Lalle sallar da ta fi falala ita ce sallar da mutum ya yi cikin gidansa in ba sallar farilla ba)). Wannan umumin za a kebanta shi da hadithin Abuu Zarr, watau sai a sake yin togo a ce: "In banda sallar Taraawiihi da sallar Ta'aqiibi cikin goman karshe na Ramadan". Musamman ma idan aka san cewa da ma can akwai wasu sallolin da aka toge su aka fidda su daga umumin wannan hadithi na Zaidu Dan Thaabit, watau kamar: Sallar Idi, da Sallar Kusuufi, da Sallar Istisqaa'i, dukkan wadannan salloli duk da kasancewarsu ba salloli ne na farilla ba toh amma kuma ba a cewa yin su cikin gidaje shi ne ya fi falala. ************************** Haka nan shi ma fitar mata zuwa wadannan salloli na Qiyaamullaili cikin goman karshe na Ramadan shi ne ya fi falala ba wai yin sallolinsu cikin dakunansu ba kamar yadda wasu mutane ke tsammani, saboda abin da ya tabbata na cewa cikin wadannan kwanakin Annabi mai tsira da amincin Allah yana tattaro 'ya'yansa mata, da kuma matansa da sauran mutane zuwa masallacinsa domin ya yi musa salla. Ke nan hadithin: ((Kada ku hana matanku zuwa masallatai, toh amma dakunasu su suka fi alheri gare su)). Shi ma hadithin Abuu Zarr ya khassasa shi, watau sai a ce: Wannan hukuncin bai shafi sallolin dare na goman karshe na watan Ramadan ba, saboda a cikinsu kam abin da ya fi falal shi ne: Matan su fita zuwa masallatai domin su yi sallolin dare cikin jama'ah a cikinsu, kamar yadda Shari'ah ta umurce su da su fita zuwa masallatan idi domin su yi sallar idi cikin jama'ah, kuma hakan shi ne ya fi falala da zama alheri a gare su a kan su zauna cikin dakunansu su yi sallar, saboda Imamul Bukhari ya ruwaito hadithi na 351, da Imamu Muslim hadithi na 890 daga Ummu Atiyyah ta ce: ((Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya umurce mu da mu fidda mata cikin idin karamar salla, da idin babbar salla: 'yan mata, da masu haila, da ma'abuta khuduuri (matan sure) toh, amma su masu haila sai su nisanci salla, su halarci alheri da addu'ar Musulmi. (ta ce: sai) na ce: Ya manzon Allah! Daya daga cikinmu ta yiwu ba ta mallaki mayafi ba? Sai ya ce: Sai 'yar'uwarta ta ba ta aron mayafi)). Intaha. *********************************** Toh amma a sauran watannin sheka da kuma kwana ishrin din farko na watan Ramadan, mutum ya yi qiyaamullailinsa shi kadai a cikin dakinsa wannan shi ne ya fi falala, saboda umumin hadithin Sahabi Zaidu Dan Thaabit Allah Ya kara masa yarda tare da sauran Sahabban Manzon Allah mai tsira da aminicin Allah. ********************************* Muna rokon Allah da ya ba mu damar cin moriyar wadannan darairai goman karshe na wannan wata mai albarka, ya azurta mu mu da iyalanmu da yin sallar Taraawiihi da Ta'aqiibi cikin jama'ah cikin masallatanmu. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 32 · November 23, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853