HUKUNCIN FADIN DA TURA SAKON (JUMA'AT MUBARAK)

Tambaya? Assalamu Alaikum. Dr ko ya halatta Musulmi yayi wa dan'uwansa murna da zagayowar juma'a ta hanyar sako a wayar sailula kamar ace JUMA'A KAREEM ko JUMA'A MUBARAK? Allah yaqara sani. Amsa: Wa alaikum assalam, Akwai malaman da su ka hana hakan, suna ganin ba shi da asali a addini, Amma abin da yake zahiri hakan ya fi kama da al'ada, wannan yasa haramta shi yake bukatar Nassi, tun da babin al'adu da mu'amaloli a bude yake, sai abin da sharia ta haramta. Duk Wanda yake yi ba tare da ya riya cewa ibada ba ce hana shi ko bidi'antar da aikinsa yana da wuya, kamar yadda Ibnu Uthaimin ya yi nuni zuwa haka a fatawar da aka yi masa. Saidai duk da haka ya kamata kar Musulmi ya zamar da shi al-adarsa kowace juma'a, don kar wasu su fahimci ibada ne. Allah ne mafi sani 23/10/2016 DR JAMILU ZAREWA

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 75 · November 23, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853