**DUNIYAR MUTUWA**(5)

Da muka isa sama ta 2, nanma aka bude mana har muka isa ta 7, sai naga itace mafi girman sammai, sai naga tamkar rafi agabanmu, naga Mala’iku sun sunkuyas da kawunansu, suka ce: “Allahumma innaka antas-salaam waminkas-salaam tabaarakta ya zhal-jalaali wal ikraam” sai naji wani firgici, na qasqantar da kaina hawaye na zubomin, sai Allah yacewa Mala’ikun: “Ku sanya littafin bawana cikin illiyin (shine rukunin da ake sanya littafan yan Aljannah -Allah ka sanya mu cikinsu-), kuma ku maisheshi zuwa qasa, domin daga gareta na haliccesu kuma cikinta zan maishesu kuma daga gareta zan tashesu wani lokaci na daban. Sabida tsananin Firgici, tsoro, da farin ciki da Murna, ban iya cewa komai ba sai: Tsarki ya tabbata gareka, bamu bauta maka ba yanda ya kamata!. Sai mala’ikun nan suka sauko dani zuwa qasa, duk sanda muka hadu da mala’iku sai muyi masu sallama, sai nacewa Mala’ikun: shin zai yiwu nasan abinda ya faru da gangan jikina da iyalaina? Sai sukace: jikinka dai zaka ganshi, amma iyalanka ayyukansune kawai da zasu dinga maka kyautarsu zasu dinga riskarka, amma bazaka gansu ba! Suka dawo dani qasa, suka ajeni kusa da jiki na, sukace: ka kasance a jikinka, mu aikinmu ya qare anan, bayan an sanyaka a qabarinka, wasu Mala’ikun 2 zasu zo maka! Sai nace dasu: Allah maku Albarka, ya saka maku da Alkhairi! To amma zan sake ganinku kuma? Sai sukace: A ranar Qiyaamah zamu tsayu gaba daya, wannan shine ranar halatta (domin dukkan mutane, Aljanu da mala’iku zasu halacce ta), sai naga sanda suka ambaci qiyamah sautinsu ya chanza, sannan sukace: Amma in ka kasance cikin yan Aljannah, zamu zamo tare ku zaka gammu. Nace: to bayan naga Aljannah kuma naji sautin ababen cikinta, shin akwai sauran shakku agareni (na zan shiga ko za’a korani wuta)? Sai sukace: Lamarin Shiga Aljannah lamarine da Allah kadai ya mallakeshi, kuma kai ka samu karramawa sabida ka mutu musulmi, abinda yayi saura shine a nuna maka ayyukanka (a qabarinka da qiyamah) da kuma mizani! Sai fuska ta ta chanza har na kusa kuka, domin ina tuna zunubaina tamkar manyan duwatsu! Sai suka ce dani: Ka kyautata zatonka ga Ubangijinka, kuma ka qudurce cewa Ubangijinka bai zaluntar kowa, Sai sukai min sallama, sukai sama da sauri….. Naga jikina akwance, sannan sai naji sautin kuka, sautine da na sanshi, Mahaifinane me qaunata da kuma dan-uwana, -subhaanallah, ina nakene yanzu?- sai na kalli jikina naga ana zuba masa ruwa, sai na gane cewar yanzu ana wanke gaawa ta ne! Sautin kukan nan na matuqar takuramin, amma duk sanda naji Mahaifina na cewa: “Allah ya sassauta maka, Allah maka rahmah” sai naji tamkar ana zubamin ruwan sanyi ne, sai suka rufe jikina da farin likafani. Sai nace cikin raina: KAICONA ACE MA BAN TABA BARIN MINTI 1 BA A RAYUWATA FACE CIKIN AMBATON ALLAH, KO SALLAH, KO WATA IBADAH! Kaicona ace ina sadaqa dare da rana, kaicona kaicona! Babban burina shine qabari, da abinda zai biyo bayansa, sai naji mai min wanka na cewa: shin zaku masa sallah ne bayan La’asar? Babana yace: Eh insha Allah -cikin kuka-! Suka dauki gaawata, ina kallonta amma bana iya magana ko motsi, suka shigar dani firij da ake sanya gaawarwaki, chan sai naji ana cewa: ku daukeshi ku kaishi masallaci! Suka daukeni inajin duk maganganunsu, babban abinda ya fi damuna shine kukan Mahaifina, kamar ince masa: kada ka damu yaa Baba, abinda ke wajen Allah yafi Alkhairi! Don Allah kabar kuka, domin ina shan radadi a dalilin kukanku, amma ko na fadi bazasu jini ba! Inajin sautukansu kuma ina gane muryar kowa, yan’uwana, kuma duk ina jin maganganunsu! Suka isa masallaci suka ajeni, sukai sallar la’asar, nai kwadayin dama ace ina taredasu muyi sallar nan nima nasamu lada! Chan bayan idar da sallah sai naji ladan na cewa: Jama’a kuzo muyiwa dan-uwanmu sallah! Bayan liman ya soma sallah, sai ga Mala’iku 2 sun zo, daya na tambayar dayan adadin masu mani sallah, nawane cikinsu muwahiddai basu hada Allah da wani? Suna rubutawa! Bayan kabbara ta 3, wacce cikinta ake mani Addu’a, sai naga mala’iku na rubuta abubuwa masu yawa, sai nasan suna rubuta Addu’o’in jama’a ne! Nai fatan dama ace liman ya tsawaita wannan kabbara kada yayi ta 4, domin har na soma sararawa ina jin dadi! Sai yayi kabbara ta 4 yayi sallama! Suka daukeni suka kaini Qabarina…………­….. Mu hadu a na 6 don jin yanda zata kasance a Qabari.

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 169 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853