**DUNIYAR MUTUWA**(02)

Bayan gama wayata da mataata, tunani ya tarun-min a raina, damuwata ta dinga qaruwa, na shiga zurfin tunani, ban Farka ba sai ji nayi Direba na Tambayata: Wai shin Yaranka nawa ne? Nace: 4, 2 maza 2 mata. Yace: Allah ya shiryar maka dasu! Nace: Amin, kaima haka. Na kalli hanya, sannan na kalli sama ina kallonta, na kalli rana, sai naga kadan ya rage ta faadi, na fadi ina mai qura kallo: Ya Allah, Rahmarka nake kwadayi yaa Rahmaan yaa Raheem! Ban Aune ba naji direba na neman izinina wai yanaso ya kunna sigaari, sai nace: Ya kai dan’uwana, kai mutum ne me daraja, kuma ina tsammanin tattare dakai akwai Alkhairi mai girma, ya zaka yardarwa kanka ka qona kanka? Ka qona kudinka? Kuma ka tauye Addininka a dalilin Sigaari? Kuma a qarshe bata amfaanarka sai dai cutar dakai??? Sai yace: Yaa kai dan Halal, kamin Addu’a, wallahi nayi qoqarin barin shanta cikin Ramadan da ya gabata amma na kasa. Sai nace dashi: kai mutum ne da Allah ya bashi iko amma ka kasa akan sigari??!! Naci gaba da masa nasiha da shiryar dashi, shi kuwa yana saurarena, yana mai nadamar shan sigaari da yakeyi, bayan kammalawata sai yace: Inshaa Allah daga yau bazan sake shan sigaari ba! Nace masa ina mai farin ciki: Allah ya Tabbatar damu akan Addini! Kawai nidai zan iya tuna cewa: na jingina kaina jikin qofar motar ina tunani, na rasa menene yasani nake firgici,na rasa akan menene, gashi inajin damuwa mai tsanani a wannan lokaci, Kwatsam!!! Sai jin qara mai tsanani nayi, gaba daya ni da direba muka rikice, nasan cewa Taaya ce ta fashe, sai nace ya rage sauri, ka sanya alama (Signal) don sauran motoci susan mun samu matsala ne, shi kuwa ko magana baya iyawa, ya kankame sitiyaarin motar, Alamun damuwa cike da Fuskarsa, lokaci qanqani motar ta hantsila bangaren daama (tabi Wrong way) ta dinga qundun baala, nidai Allah ya taimakeni inata fadin “Laa ilaaha illallaah, Muhammadur-Rasululla­ah” inajin kamar ina daga muryata da ita ne, bayan nan naji wani duwka mai qarfi ta qasan kaina, naji tamkar harshen wutane sabida tsabagen zaafinta! Motar ta wuntsula ba adadi, hardai ta tsaya, a nan ne nayi yunqurin fitowa in miqe, amma na kaasa, na kaasa koda motsa ga6a 1 ta jikina, naji wani irin radadi wanda ban tabajinsa ba a rayuwata, na kaasa magana, idanuwana a bude suke, amma bana iya ganin komai in banda duhu! Chan sai naji sautin takalman mutane na gabatowa kusa da mu, ina ji suna cewa: kada ku tabashi, kanshi na zuban jini qafarsa ta karye, sai na soma jin numfashi na na tsananta, naji wani irin zaafi mai tsanani na tasowa daga qafata zuwa kai na! Sai naji suna cewa: ina direban yayi ne? Sai naji wani mutum yace: kuji sautinsa chan nesa, yana neman taimakonku, mutuwa zai ba makawa baya iya motsi!!!!!!! Naji Radadin na qaruwan min, inata tunane-tunane! Shin wannan ne qarshena? Subhaanallaah! Na soma nadaama mai tsanani bisa lokutan da na baata a rayuwata, da taqaita ayyukan Alheri da na dingayi a rayuwata! Yanzu gaani a lamarinda dole mai aukuwa ne ba makawa! Sai na soma jin sautin mutane na bace min, duhu ya soma tsananta a idona, radadi kuwa tamkar ana yayyanka jikina da wuqaqe, sai naji kamar wani abu na maaqureni, yana hana iska zuwa min! Anan na tabbata rayuwata ta yanke kenan! Chan sai ga wani mutum ya zomin, cikin tsananin duhu da nake gani, yazo min da Gemuna fari Fat!!!!!!! Ku biyoni gobe da Yardar Allah don jin wanene wannan Mutumi? Me yazowa wannan Baawan Allah dashi bayan Mutuwarsa? Mai zai faru da wannan Mutumi bayan Mutuwarsa? Dan uwa shin kana shirin mutuwa, kokuwa kana tsammanin ta tsoffi ce?????

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 130 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853