**DUNIYAR MUTUWA**(01)

A daya daga cikin tadfiye tafiye na zuwa Birnin Riyaad, nai shirin zuwa filin jirgin sama kafin lokacin tashin Jirgin da Awa 1, sai dai cunkoson hanyar, da kuma Bincike yasa na makara a tafiyata, sai na dinga sauri har na isa wajen tsayuwar motoci, sai na dauki Kaati na (Visa) da sauri, nai Parking motata a wurinda ni bansan shin wurin Parking din ma’aikata ne ko na matafiya, ni dai na sauko da sauri daga mota na dauki Jakaata a hannuna, na shiga abin tafiya (Escalator) na isa dakin bincike, na cire duk abindake aljihuna na riqe a hannu, na danna na’urar bude qofa, amma sai naji sanarwar cewa wai a jikina akwai wani abu da bazan iya wucewa dashi ba, sai na shiga damuwa, chan sai na tuna Agogona ne ai, sai na cire, na sake danna na’urar, sai ta bude na wuce lafiya. Na isa wajen mai bada Tikitin Jirgi da sauri, nace: Ni matafiyi ne zuwa Riyaad, cikin jirgi mai lamba 1411, sai ma’aikacin yace: Ai Jirgin ya cika, sai nace dashi: Don Allah ka taimakamin, inada Alqawarine wanda ba makawa in halarceshi a wannan Dare. Sai yace: Kada ka yawaita magana, don Jirgi ya riga ya cika, kuma babu wanda zai daga maka qafa, sai nace: Hasbiyallah!!!! Na fito daga wajensa, na tsaya ina kallon jirgin banida tsimi banida dabaarah face ga Allah, sai tunani yadinga ketomin akaina cikin sauri! Shin zan bar tafiyar nan ne? Kodai in tafi a Motata? Ko in dauki hayar mota in tafi? Sai dai zuciyata ta bani in tafi a motar haya, sai na koma bangaren yan Tasi (Taxi), sai na samu wani mutum cikin sabuwar Mota (Camry), na ce dashi: Nawa zaka kaini Riyaad? Yace: Riyal 500! Nayi qoqarin samun ragi wajensa, amma bai ragen komaiba illa Riyal 50. Na hau Motar ni kadai, nace dashi yayi sauri, domin dolene na Isa Riyaad cikin wannan Dare, ni ban sani ba, ashe qarshena cikin Awanni ne!!!!!!!! Yace dani: Sha Kuruminka, zanyi gudu dakai tamkar Tsuntsu, ai kuwa haka akai, ya dinga gudu na hauka, don na masa Alqawarin idan ya isa Riyaad dani kafin Isha’I, zan bashi qarin kyautar Riyal 100 (bayaga 450 dinsa). Muna tafe muna hira yana tambayata ina tambayarsa muna raha, don dai mu debe kewar juna! Kwatsam sai mahaifiyata ta fadomin qwaqwalwata akan in kiraata, ai kuwa na kirata, tace: Ina kake ne ya Aba-Saarah? Sai na bata Labarin Jirgi, da yanda na rasa tafiya ta Jirgi, sannan yanzu na hau mota ne don tafiyar, sai tayyi shiru, wanda hakan ya janyo hankali na, sai mhaifiyata tace: Ka kula ya kai Daana, Allah kareka daga sharrin abindake boye, sai nace: Amin, zan kiraaki da zaarar na isa Inshaa Allah, kinada wasiyya gareni ne? Tace: kasancewarka Lafiya ya Tsayin Rayuwata!!!!!!……­.. Anan muka kammala waya da ita! Sai naji wani abu a raina, nakejin wani abin Al-ajabi na shirin Aukuwa dani! Sai na kira Mataata, tace: Bani Labarinka ya rayuwata, Kilomita nawa kukai? Nace: Yanzu munyi Kilomita 150. Tace: Wallahi munyi rashinka, in baka gidannan duk babu dadi! Nace: Allah ya maki Albarka, in Allah yaso inanan dawowa a jirgin Raana, ki kula da yaara na, ki sumbancemin Susu, Allah ya kula mana da ita! Tace: albishirinka, ai tun randa ta dawo take ina Baba? Nace: Bani ita! Susu tace: Baba ina kake? Nace: Susu nan bada jimawa ba zan dawo maku inshaa Allah, muka danyi dariya nace to ba Mama wayar, sai ta bata, nace: kinada wata wasiyyace gareni? Tace: Fataana shine kubutar rayuwarka! Ban sani ba menene dalilinda yasa damuwa ta soma tsananta agreni! Na shiga Zurfin tunani wanda ban dawo ba sai ji nayi Direba na Tambayata………..­………. Ko me Direban ya Tambayeshi? Shin ya zasu qarke a hanya, yana isa Riyaad kuwa???? Mu hadu gobe da yardar Allah.

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 130 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853