SHIN BAIKO AURE NE ?

Tambaya : Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai yi tafiya ya biyo ta gidanmu wai yana so mu sadu, ya yi ta kawo min kauli da ba'adi, ni dai gaskiya malam na ki yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ? Amsa; To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa a Nigeria cewa : baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure ba ne saboda hujjoji kamar haka : 1. Abin da aka sani shi ne kudin da ake ba da su yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunkulewa su bayar gaba daya, kin ga kuwa in haka ne, to ai dukkan aiyuka ba sa ingatuwa sai da niyya, kamar yadda ya zo a hadisi da dukkan malaman hadisi suka rawaito. 2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a dawo masa da kudinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne. 3. Hakan zai iya bude hanyoyin barna, don dukkan wani ashararu zai iya kai kudi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa barna. 4. Yana daga cikin sharudan auren a wajan wasu malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kudin da za'a yi baiko, zai iya zama mutum daya, kin ga akwai nakasu kenan. 5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an yi baiko, ake sanya ranar daurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko daban, aure daban. 6. Sannan duk mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado tsakanin tsakanin wadanda aka yiwa, idan daya daga cikinsu ya mutu ka ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne, domin ma'aurata suna gadon junansu . Allah ne ma fi sani

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 134 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853