((ALAIKUM BI SUNNATI WA SUNNATIL KHULAFAA'IR RAASHIDIN)) ((عليكم بسنتي وسنة الخلفاء الراشدين))

1. Wannan hadithin yana nufin wajibi ne a bi sunnar Khulafaa'ir Raashidin a lokacin da ita sunnar Khulafaa'ir Raashidin din ba ta yi karo da wani nassi na Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ba; saboda babu ma'asuumi cikin Khulafaa'ur Raashidun, Annabi mai tsira da amincin Allah shi kadai ne ma'asuumi, duk wani wanda ba shi ba cikin wannan Al'ummah yana iya yin daidai kuma yana iya yin kure, wannan shi ne aqidar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah, sabanin wasu 'yan bidi'ah da suke cewa shugabanninsu ma'asuumai ne tamkar yadda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yake! 2. Da za a kaddara cewa za a sami wata fatawar da daya daga cikin Khulafaa'ur Raashidun zai yi, sannan kuma a sami wani nassi daga Manzon Allah mai tsira da amincin Allah da yake saba wa wannan fatawar to dole ne a bar wannan fatawar a koma a yi aiki da maganar Annabi mai tsira da amincin Allah. 3. Domin taimakon 'yan'uwa fahimtar wannan bayani da muka yi a sama ga wasu fatawowi daga cikin fatawowin babban malami a duniyar Ahlus Sunnah Wal Jama'ah watau Sheikhul Islam Ibnu Taimiyah. Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202:- ((واما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)). Ma'ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan'bidi'ah ne, kai kafiri ne ma)). Sannan ya sake cewa cikin littafin 27/125:- ((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)). Ma'ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma'asuu'mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma'asuu'mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)). Sannan ya sake cewa a cikin littafin 20/251:- ((وليس لاحد ان يعارض الحديث عن النبي صلى الله عليه وسلم بقول احد من الناس كما قال ابن عباس رضي الله عنهما لرجل ساله عن مسالة فاجابه فيها بحديث فقال له: قال ابو بكر وعمر فقال ابن عباس: يوشك ان تنزل عليكم حجارة من السماء اقول لكم قال رسول الله صلى الله عليه وسلم وتقولون قال ابو بكر وعمر)). Ma'ana: ((Babu wanda yake da damar ya kalubalanci Hadithi daga Annabi mai tsira da amincin Allah saboda maganar wani mutum daga cikin mutane, kamar dai yadda Dan Abbas Allah Ya kara musu yarda ya ce wa wani mutumin da ya tambaye shi game da wata mas'ala' sai ya ba shi amsa da wani hadithi, sai mutumin ya ce da shi: Amma Abubakar, da Umar kuma sun ce!! Sai Dan Abbas ya ce: Duwatsu sun yi kusa su sauko a kanku, ina cewa da ku Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce, sannan ku kuma kuna cewa: Abubakar da Umar sun ce))? Muna rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya tausaya mana Ya cusa son Annabi da son bin sunnarsa cikin zukatan al'ummarmu. Ameen. DR IBRAHIM JALO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 20 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853