MUNA TSARKAKE IMAM MALIK DAGA KARKATAR KARKATATTU:

Muna tsarkake Imam Malik daga irin abin da wasu karkatattu suke son su nuna wa jama'a cewa shi ne matsayin wannan babban Malami cikin duniyar Musulmi. Lalle irin abin da wadannan karkatattu suke yi abin takaici ne matuka. Na'am Bin Bazz ba hujja ba ne akan Imam Malik, amma shi Annabi mai tsira da amincin Allah hujja ne a kan shi Imam Malik da ma wanin Imam Malik, ke nan maganarsa da aikinsa shi ne za a bauta wa Allah da shi ba wai da abin da imam malik ya yi ko ya fada wanda ya saba da na Annabi za ayi aiki da shi ba, matukar dai Muduluncin ne za a yi ba wanin shi ba. Kaddara Imam Malik ya yi wani abu da ya saba wa abin da Annabi ya yi ko abin da Annabi ya yi umurnin a yi, ai ba wani abin mamaki ba ne saboda ai shi ba ma'asumi ba ne, sannan kuma ba dukkan hadithan Annabi ba ne ya sani. Sannan abin da Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce shi ne: "Ku yi salla kamar yadda kuke gani na nake yin salla". Babu inda shari'ah ta ce: Musulmi su yi salla kamar yadda Imam malik yake yin salla. Abin bakin cikin mai amsa sunan musulmi a ce da shi: Annabi ya ce sannan shi kuma ya koma yana cewa: ai malam wane ma ya ce!! Allah ka tsare mana biyayyarmu ga Annabi Muhammad. Ameen. DR IBRAHIM JALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 10 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853