DARE SHI NE FARKO SANNAN YINI YA BIYO BAYA:

Ya kamata a san cewa tun lokacin da aka ga Wata ne Ramadan ya shigo, ba wai sai da gari ya waye ba tukun. Jiya an ga jinjirin Wata ne a lokacin da yinin Lahadi ya wuce; watau bayan Rana ta fadi, da kuma faduwar Rana ne daren Litinin ya shigo, dama kuma yadda ka'idar take shi ne: Dare shi ne farko sannan Yini ya biyo baya, haka wannan lamari yake cikin dukkan Addinai da Annabawa suka zo da su. Kure ne babba a ga Wata sannan wani ya ce: Mun ga wata yau Lahadi, gobe Litinin daya ga Watan Ramadan! Kuma abin bakin ciki shi ne wannan kure ya zan abin riko da aiki da shi cikin Jama'a, haka za ka rika jin 'yan jarida na maimaita shi, kai har ma da Sarakuna, da wasu daga cikin shugabannin Addini! Allah Ka ba wa shugaban kasarmu lafiya, Ka kuma ba mu dukkan alkhairan da ke cikin wannan Wata na Ramadan. Ameen. DR IBRAHIMJALO JALINGO

by: Hassan Auwalu Ya'u. · 10 · November 20, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853