DUNIYA MAKARANTA FITOWA TA HUDU

16. Rayuwa kamar kasuwa ce. Ka zagaya ka tsinci duk abin da ka ke so. Idan ka zo fita za ka biya duk abin da ka dauka. 17.Wanda bai iya karatu da rubutu ba jahili ba ne! Amma wanda ya fi shi jahilci shi ne wanda ya san gabas amma kuma ba ya sallah!! 18. Idan ka mutu an rufe labarinka, amma abubuwa uku suna rayuwa a bayanka: a. Ilimi b. Haifuwa c. Aikin alherin da ka shuka 19. Abokai iri uku ne: a. Mai son ka don abinka. b. Da mai sonka don kanka. c. Da mai son ka don kansa. Irin wannan yana tare da kai ne idan ka samu. Iidan ka rasa zai yi ko-sama-ko-kasa. 20. Idan ka yi fushi ka kama bakinka. Domin ba kai ne za ka yi magana ba a lokacin, shedan ne! Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 332 · August 09, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853