DUNIYA MAKARANTA FITOWA TA UKU B

Fitowa ta 3b 11. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudun su ake yi. Wasu kamar magani suke, akai akai bukatar su. Wasu kuma kamar abinci suke, a kullum dole ne a neme su. Yi kokari ka zama wanda a kullum ake neman sa saboda amfaninsa. 12. Idan ka kwanta ba ka sani ba wane ne zai tashe ka? Iyalanka ne ko Mala'ikan mutuwa?! Zama cikin shiri a kullum don kada a riske ka. 13. Ana yin da-na-sani a kan magana, amma ba a cika yi a kan kawaici ba. Kama bakinka duk lokacin da ba ka tabbatar da amfanin magana ba. 14. Kada ka damu da masu kulla ma ka sharri, duk iya kokarinsu ba su wuce zartar da kaddarar Allah a kan ka. 15. Alamomin tsoron Allah guda biyar ne: a. Fadin gaskiya b. Cika alkawari c. Rikon amana d. Jin tausayi da e. Kyautata ma mutane. Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 203 · August 09, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853