DUNIYA MAKARANTA FITOWA TA UKU A

MASU HIKIMA SUN CE 11. Allah yana karbar aikin duk wanda ya girmama shi, matukar bai yi wa bayinsa giraman kai ba. 12. Gwanintar mai dafa abinci da zakin miya ba su ke sa abinci dadi ba, lafiya ce ta ke sa a ji dadinsa. 13. Kazantar jiki da wahalar da shi ba shi ne tsoron Allah ba. Tsoron Allah shi ne bin umarninsa da barin haninsa. 14. Mai tsoron Allah bai damu da duniya a hannun wa ta ke ba. 15. Duniya kamar macije ce. Jikinta da kyau da laushi, amma gubarta mai kisa ce. Ku rabu da ita don karancin abin da za ku tafi da shi cikinta in za ku kabari. Littafin: Sheikh Baba Ahmad As-Shinkidi Fitarwa da gyarawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 400 · August 09, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853