DUNIYA MAKARANTA FITOWA TA BIYU

BISMILLAHIR RAAHMANAR RAHIM 11. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudun su ake yi. Wasu kamar magani suke, akai akai bukatar su. Wasu kuma kamar abinci suke, a kullum dole ne a neme su. Yi kokari ka zama wanda a kullum ake neman sa saboda amfaninsa. 12. Idan ka kwanta ba ka sani ba wane ne zai tashe ka? Iyalanka ne ko Mala'ikan mutuwa?! Zama cikin shiri a kullum don kada a riske ka. 13. Ana yin da-na-sani a kan magana, amma ba a cika yi a kan kawaici ba. Kama bakinka duk lokacin da ba ka tabbatar da amfanin magana ba. 14. Kada ka damu da masu kulla ma ka sharri, duk iya kokarinsu ba su wuce zartar da kaddarar Allah a kan ka. 15. Alamomin tsoron Allah guda biyar ne: a. Fadin gaskiya b. Cika alkawari c. Rikon amana d. Jin tausayi da e. Kyautata ma mutane. 16. Rayuwa kamar kasuwa ce. Ka zagaya ka tsinci duk abin da ka ke so. Idan ka zo fita za ka biya duk abin da ka dauka. 17.Wanda bai iya karatu da rubutu ba jahili ba ne! Amma wanda ya fi shi jahilci shi ne wanda ya san gabas amma kuma ba ya sallah!! 18. Idan ka mutu an rufe labarinka, amma abubuwa uku suna rayuwa a bayanka: a. Ilimi b. Haifuwa c. Aikin alherin da ka shuka 19. Abokai iri uku ne: a. Mai son ka don abinka. b. Da mai sonka don kanka. c. Da mai son ka don kansa. Irin wannan yana tare da kai ne idan ka samu. Iidan ka rasa zai yi ko-sama-ko-kasa. 20. Idan ka yi fushi ka kama bakinka. Domin ba kai ne za ka yi magana ba a lokacin, shedan ne! Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto Darulfikr Islamic Data Bank where you can get free access to unlimited Articles, Events, Motivations and Download, Play or share Audio files by Hausa / English scholars. Hassan Auwalu Ya'u Hussaini Auwalu Ya’u Facebook: https://fb.com/hussainiauwaluyau Instagram: hussainiauwaluyau01 Twitter: Hussainiauwalu1 Email: hussainyau01@gmail.com Contact: +2348149332007 ⋕Hussainiauwaluyau

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 268 · August 09, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853