DUNIYA MAKARANTA FITOWA TA DAYA

DUNIYA MAKARANTA 1 Rubutawar : Dr Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto Bugu Na Biyu Bugawa Da Yadawa : Bugu Na Farko 1437 AH =2016 Hakkin Mallaka @Mawallafi mansursokoto@yahoo.co.uk ISBN 9960-49-972-3 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM GABATARWA Yabo Da Godiya Da’iman Wa Abadan Na Allah Ne. Salati Da Sallama Su Ne Na Fiyayyen Halitta, Shugaban Annabawa Kuma Jagoran Manzanni Annabi Muhammad, Da Iyalan Sa Da Sahabbansa Baki Daya. Wadannan Kalmomi Na Rubuta Su Ne Don Amfanin Kaina Da Kuma Jama’a Game Da Darussan Da Wannan Rayuwa Take Dauke Da Su. Kuma Tasharmu Mai Farin Jinni Ta wisalhausatv Tana Ci Gaba Da Yada Shi Kullum Safiya Ta Allah. Haka Kuma Ana Yada Wadannan Kalmomi Masu Amfani A Shafin Minbarin Malamai Wanda Yake Group Ne Na Fadakarwa A Whatsapp Wanda Ya Kunshi Darussa Da Fa’idoji Masu Amfani ⪧ Wadanda Suke Son Shiga Wannan Azure Za Su Iya Aika Lambobin Su Ta Whatsapp Ga 08064661666 Ko Kuma Su Aika Da Text Message Zuwa Ga 09030606028. Na Samu Kwarin Gwiwar Ci Gaba Da Rubuta Wadannan Hikimomi Wadanda Nike Zakulo Su Daga Alkur’ani Da Hadisai Da Maganganun Masu Ilimi Da Basira Da Fahimtar Rayuwa Na Da,Da Na Yanzu. Abin Da Ya Bani Kwarin Gwiwar Kuwa Shine Na’am Da Masu Karatu Suka Yi Da Su. Abin Da Ya Nuna Cewa ,Kamar Yadda Nike Karuwa Da Su , Haka Sauran Jama’a Su Ma. Wannan Kashi Na Farko Ne , Kuma Insha Allahu Za Mu Rinka Fitar Da Su Akai-Akai Har Iya Inda Allah Gwanin Sarki Ya Bamu Iko. Baban Ramla A Sakkwato 27 Ga Safar 1437 AH BISMILLAHIR RAAHMANAR RAHIM 1. Sauki yana tare da tsanani. Mai hakuri yana cim ma dadi. Mai kyauta ba ya rasawa. Kowa ya ji tsoron Allah, Allah zai yi ma sa mafita. Manta da damuwa ka fuskanci rayuwa. Kowa ka gani a duniya akwai abin da ya dame shi. 2. Idan za ka yi alheri ka gaggauta shi, ka sirranta shi, sannan kada ka yi gori. Wannan shi ne halin mutanen kirki!. 3. Idan ba ka iya yin sadaka daga abin aljihunka to ka yi sadaka daga cikin hakoranka. Murmushi ga fuskar dan uwanka shi ma sadaka ne. 4. Ba kowane aiki ne karfi yake yi ba. Wani aikin hakuri ne yake yin sa! 5. Yaro akwai lokaci da karfi amma babu kudi. Dattijo akwai kudi da karfi amma babu lokaci. Tsoho akwai kudi da lokaci amma babu karfi. A rayuwa in ka samu wani abu ne za ka rasa wani. Cikakkiyar ni'ima kawai tana aljanna. Ya Allah ka ba mu aljanna. 6. Makiyanka mutane uku ne: Mai kin ka, da mai kin masoyinka, da mai son makiyanka. Mai son uwa dole ya so danta. 7. Macce ce ta haife ka. Macce ce ta yi rainon ka. Macce ce kuma uwargidanka. Ta ya ya za ka raina macce? 8. Uwa ita kadai ce take manta kanta a addu'a, ta shagaltu da yi ma danta. Mu so iyayenmu. 9. Abubuwa uku ne su ke kawar da bala'i: Sadaka da Addu'a da sada Zumunta. 10. Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa: Magana da Lokaci da Mutunci. Rubutawa: Dr. Muhammad Mansur Ibrahim Sokoto Darulfikr Islamic Data Bank where you can get free access to unlimited Articles, Events, Motivations and Download, Play or share Audio files by Hausa / English scholars. Hassan Auwalu Ya'u Hussaini Auwalu Ya’u Facebook: https://fb.com/hussainiauwaluyau Instagram: hussainiauwaluyau01 Twitter: Hussainiauwalu1 Email: hussainyau01@gmail.com Contact: +2348149332007 ⋕Hussainiauwaluyau

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 1,309 · August 09, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853