KA KOYI LADABIN ILIMI KAMAR YANDA KAKE KOYAN ILIMI.

Assalamu alaikum Magabata na kwarai sun kasance suna fifita ladabin ilimi akan ilimi,suna fara koyan ladabin malamansu kafin su koyi ilimi awajan su,kuma suna koyan ilimi tare da labadi da halaye masu kyau na malaman su,sai hakan ya sanya Allah ya sanyawa ilimin su albarka mai yawa. Wannan shine babban bambanci tsakanin masu ilimi na magabata da masu ilimi na wannan zamani,mafi yawancin masu neman ilimi na yanzu muna neman ilimin ne kadai ba tare da ladabi da tarbiyya ba,zaka sami Dalibin ilimi ga ilimin amma a bangaran ladabi da tarbiyya zero yake kai kace a Tasha ya koyo ilimin,babu girmama ilimin babu girmama malaman da yake koyan ilimin a wajansu,mafi yawansu ma suna barin wajan neman ilimin ne saboda jayayya da malaman su da kuma raina su,sai kaji suna cewa malaman bai iya Nahwu ba baya da balaga da dai sauransu. *Maganganun magabata na kwarai ladabi* إبراهيم بن حبيب - رحمه الله; *"Yana yi ma dansa wasiyya sai yake ce masa;Ya kai dana, katafi neman ilimi wajan malaman Hadisi da Fiqhu,amma ka koyi ladabin su da kyawawan halayensu kamar yanda zaka dauki ilimi a wajan su,domin ka koyi ladabinsu da kyawawan halayensu shine mafi soyuwa a garesu fiye da yawan ilimi da zaka koya babu ladabi da kyawawan halaye"* @الجامع للخطيب(1/ 80). الإمام مالك بن أنس رحمه الله تعالى; Yana cewa: *"Mahaifiyata ta kasance tana cewa dani;kaje wajan RABI'AH,ka fara kowan ladabinsa kafin ka fara koyan iliminsa"* @ترتيب المدارك وتقريب المسالك (130/1) عبدالله بن المبارك رحمه الله تعالى: Yana cewa: *"Na nemi ladabin ilimi da malamai tsawon shekara talatin,na kuma nemi ilimi tsawon shekara ashirin,magabata sun kasance suna koyan ladabin ilimi dana malami kafin su fara neman ilimi"* @غاية النهاية في طبقات القراء (1/ 198). Wani dalibin Imam Ahmad yana cewa: *"Mun kasance muna haduwa a wajan daukar karatu a wajan Imam Ahmad bn Hambal mu sama da dubu biyar,mutum sama da dari biyar suna rubuta darasi sauran kuma suna koyan kyawawan halaye da ladabi a wajansa"* @السير (2/ 947). ابن الجوزي : رحمه الله تعالى Yana cewa: *"Koyan ladabin ilimi da ladabin malami yana daukar kashi biyu cikin uku na ilimi"* @صفة الصفوة 4/ 145 عبد الله بن المبارك رحمه الله تعالى; Yana cewa; *"Mu a wajan mu muna ganin koyan ladabin ilimi da ladabin malami komai kadan dinsa yafi alkhairi akan yawan ilimi"* @مدارج السالكين (2/ 376) عبد الله بن وهب رحمه الله تعالى-: Yana fada; *"Mun koyi ladabin imam Malik fiye da yanda muka koyi ilimi a wajansa"* سير أعلام النبلاء (8/ 113) Allah ne mafi sani. Rubutawa Sheikh Aliyu Said Gamawa

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 405 · August 09, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853