Lamiyatu Sheikul Islam Ibn Taimiyya

Lamiyatu Sheikul Islam Ibn Taimiyya Kasida Ce Da Ta Kunshi Akidar Ahlussunnah Waljama’a game da: Akidar su game da Allah Akidar su game da Al-kur’ani Akidar su game da Annabi (s.a.w) Akidar su game da Sahabban Annabi (s.a.w) Akidar su game da Iyalan Gidan Annabi (s.a.w) Akidar su game da Ranar Tashin Alkiyama da Abubuwan da zasu faru a Wannnan Rana Duka wadannan Bayanai na Kunshe Cikin Littafin ne Don a Ban-Bance Akidar Ahlussunnah Waljam’a da wadanda basu ba,Domin Idan Ance Ahlus-sunnah ba’ana nufin mutane ne wadanda suka sha ban-ban ta fuskar yare,gari ko launin fata ba, A’a sun sha ban-ban da sauran Akidu ne ta hanyar kudurin zuci da maganar baka da kuma Aikin gabbai, wannan shi ya ban-ban ta Ahlussunnah da sauran mutane wadanda basu ba. Kuma Ana kiran su da suna Ahlussunnah don ban-ban tasu da sauran ‘yan Bidi’a, Don su kai tsaye suna dangantuwa ne ga sunnar Manzon Allah (s.a.w). Sukan ‘yan Bidi’a sun fi so a danganta su ga wani mutum ko wani gungu na mutane wanda ba Manzon Allah (s.a.w) ba. Misali ka Dauki Akida ta shi’anci: Gungun wasu mutane ne da suke nuna fifikon Sayyadina Aliyu (R.A) Akan dukkan sauran sahabbai, Haka Idan ka dauki Akidar Tijjaniyya suma wasu gungu ne na mutane dake Bin wani mutum wai shi Sheikh Ahmad Tijjani wanda suma Akan haka suke rayuwa kuma suke kiran mutane Akan su zama Akan haka, Haka zalika Idan ka dauki kadiriyya zaka ga dangantuwar gun-gun wasu mutane ne zuwa ga wani mutum Sheikh Abdulkadir suna yin nisba zuwa gareshi kuma shine abun alfaharin su kuma shine Abun fatan su, Akan haka suke rayuwa kuma akan haka suke kiran kowa ya zama. Amma su Ahlussunnah su sai suka zama suna dangantuwa zuwa ga Annabi ne shi kadai, Ba sa dangantuwa zuwa ga wani mutum ko wani gungu na mutane, A’a komai dangantuwar wani mutum ga Annabi (s.a.w) To suna ganin Annabin dai yafi musu sama da dangantuwar su zuwa ga wani mutum koda kuwa Salihin bawa ne domin ai bai kai annabi (s.a.w) ba. Allah Ka Azurta Mu Da Fahimtar Dai Dai, Da Fadin Dai-Dai Tare Da Aikata Dai-Dai,Ya Kuma Kawar Damu Daga Sharrin Kawu Kanmu Da Kuma Sharrin Shaidan, Sheikh Ja’afar Ya Karantar Da Wannan Kasida Mai Baitika Guda Goma Sha Biyar Tare Da Sharhi Tsaka-Tsaki Game Da Su A Masallacin Gwallaga Dake Garin Bauchi State, A Ranar Lahadi 21 Jumada Ula 1427 A.H = 18-June-2006 A Matsayin Darasi Na Musamman, Muna Rokon Ubangiji Ta’ala Yajjikan Sa Da Rahma Yasa Aljannah Ce Makomar Sa Ameen. Domin yin downloading sai ka dannan blue din rubutun dake kasa 001 LAMIYATU SHEIKUL ISLAM IBN TAIMIYYA http://darulfikr.com/s/25934 002 LAMIYATU SHEIKUL ISLAM IBN TAIMIYYA http://darulfikr.com/s/25935 Ayi Sauraro Lafiya Wadannan Jerin Karatuttukan Littattafai Sune Wadanda Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Ya Karantar Wadanda Muke Dasu , Kuma Zaku Same Su A Shafin Yada Sunnah Na Darulfikr.Com Ta Hanyar Bin Wannan Link: http://darulfikr.com/m/scholar/jaafar-mahmud-adam Cikakken Tafseer Na Alku’ani Mai Girma Arba’una Hadith Kitabut Tauhid Sifatu Salatin Nabiyyi (S.A.W) Umdatul Ahkam Inda Mal Ya Tsaya Tambayoyi Da Amsoshin Su Guda 1000 Kira’a Ta Mal Ja’afar Muhadarori Ahkamul Jana’iz Bulugul Maram Riyadus Salihin Mukhtasar Siratur Rasul Inda Mal Ya Tsaya Kashbush-Shubuhat Khudubobi 80 Halaccin Karatun Boko Da Aikin Gwamnati Wa’azuzzuka Na Fannoni Daban-Daban Balaghatul Wadhi Nahwu Adabi Al Waraqat Fi Usulul Fiqhi Littattafan Da Suke Kan Hanya Sharhu Usulul Iman Tuhfatussaniyya Usulul Tafseer Ya ‘Yan Uwa Musulmi Kuma Zaku Iya Bada Gudunmawar Ku, Domin Samun Karatuttukan Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Wadanda Basu Futo Ba, Don Yada Sunnah Ta Hanyar Tuntubar Lambobi Kamar Haka 09035830253,08149332007 ⭕ Zaku iya samun darulfikr a wayoyin ku kirar Android domin more sabon karatu da zarar an saka a darulfikr.com a kyauta,Domin samun naka ziyarci PlayStore ta hanyar danna link dake kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.darulfikr.darulfikr Darulfikr.com Ta kuce Domin Yada Sunnah. Darulfikr Islamic Data Bank where you can get free access to unlimited Articles, Events, Motivations and Download, Play or share Audio files by Hausa / English scholars. Kasance Da Darulfikr Domin Samun Karatuttukan Malaman Sunnah A Saukake Basheer Journalist Sharfadi Muhd Basheer Ridwan Ammar Isa Hotoro Mubarak Auwal Mustapha Bin Adam Hassan Auwalu Ya’u Faisal Nasir Muhammad Jami’an da suka agaza wajen kawo muku wadannan Karatuttuka Domin gyara ko shawarwari kuna iya bibiyarmu ta wadannan hanyoyi: Hussaini Auwalu Ya’u Facebook: https://fb.com/hussainiauwaluyau Instagram: hussainiauwaluyau01 Twitter: Hussainiauwalu1 Email: hussainyau01@gmail.com 22-Shawwal-1437 A.H 15-July-2017 A.c #Hussainiauwaluyau

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 596 · July 15, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853