KWANAKI NAWA NE TSAKANIN HAILA ZUWA WATA HAILAR?

Tambaya: Assalamu alayk wa Rahmatullah wa Barakatuh. Don Allah kwanaki nawa ne tsakanin haila da wata hailar don yau kwana 13 da na fara haila sai na yi kwana 5 na yi tsarki sai kuma yau gashi ta zo. Allah Ya sa mu dace. Don Allah ina jiran answer don in san hukuncin da ke kai na. Its urgent pls. *Amsa:* To, 'Yar uwa, Malaman Musulunci sun hadu akan cewa shari'ar Musulunci ba ta kayyade wasu kwanakin tsawon tazarar Haila zuwa wata Haila ba, amma sun yi sabani game da karancin tazarar kwanakin Haila zuwa wata Hailar. Wasu Malaman sun ce: karancin kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Hailar, sai ya kai kwana goma shabiyar (15), wasu suka ce: kwana goma sha uku (13), wasu sukace kwana goma (10), wasu suka ce: kwana takwas (8) zuwa goma (10), wasu suka ce kwana takwas (8). Amma magana tabbatacciya ita ce Shari'ar Musulunci ba ta kayyade karanci ko yawan tazarar kwanaki tsakanin Haila zuwa wata Haila ba, Mace tana iya yin Haila uku (3) cikin wata guda musamman masu amfani da magani ko allurar tazarar haihuwa, nan da nan sai Haila ta ta zo musu. Sai dai idan Mace ta yi da'awar ta gama idda kasa da lokacin da aka saba gama idda, to sai ta zo da wanda zai shedeta cikin danginta makusanta akan cewa haka hailarta take. A duba Majmu'ul fatawah na Sheikhul Islam Ibn Taimiyya Mujalladi na 19, ko littafin Al-Haidu wal Hamdu wannifaas bainal fiqhu waddibu na Umar Sulaimanu Al- Ashqar, dan samun karin bayani. Allah ya taimake mu. Amsawa: Malam Ibrahim Jushi, Zamfara 04/07/2017. Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH

by: Mubarak Auwal · 1,208 · July 04, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853