TSARKIN HAILA YA ZO MATA GA SHI BATA DA LAFIYA BA ZA TA IYA TABA RUWA BA, YA ZA TA YI?

Tambaya: Assalamu alaikum, Mal. Mace ce ta gama haila amma a lokacin bata da lafiya kuma in har ta sa ruwa akanta akwai matsala, Yaya ya kamata ta yi?. Amsa: Wa rahmatullahi wa barakaatuhu, Idan jinin Haila ko na Biki ya dauke ma mace a lokacin da take cikin uzurin da ya hana ta amfani da ruwa to, za ta jinkirta wanka sai uzurin da ya hana ta wanka ya gushe, sai dai kafin ta yi wankan sai ta rika yin taimama madadin Alwala. A duba littafin Majmu'ul fatawah na Shaikhul Islam Ibn Taimiya mujalladi na 19, dan samun karin bayani. Allah ne mafi sani. Amsawa: Malam Ibrahim Jushi, Zamfara 01/07/2017. Daga: ZAUREN FIQHUS SUNNAH

by: Mubarak Auwal · 746 · July 03, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853