MEYASA SUKE CEWA KARATUN BOKO HARAMUN NE? HALACCIN KARATUN BOKO.

Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh Dalilan daya sanya wannan shafin namu na Darulfikr.com ya sanya wadannan karatuttuka shine sau dayawa ‘yan uwa kan dauki abubuwan da suka wuce shekaru da dama a baya su dawo dashi kamar a wannan lokacin yake faruwa, musamman idan suka san cewa su wadannan abubuwan da za’ayi ta magana akansu wanda ake jinginawa baya raye, To sannan sukan samu damar da zasu soke shi tare da jingina masa Datti da duk abunda suka ga damar su fada dangane dashi, asali kam maganganun da suke fada basu da asali ta bangaren shi wanda suke jinginawa, saboda haka sai suyi wasa da kwakwalan masu karamin tunani ko kuma wadanda basu son komai ba dangane da abubuwan da ake magana akansu. Wannan Al’ada bata tsaya kadai akan dalibai ba, ta tsallaka har zuwa maluman su wajan aikata wannan mummunar Al’ada domin a kwanakin baya ga duk ‘yan uwa dake bibiyar Al’amura irin na ban-bance – ban-bancen ra’ayoyi dan gane da abunda ya shafi akida a kasar nan, an samu shugaban wata kungiya da yayi kiran cewa ya kamata dukkan wata kungiya da dariku cewa a aje ban-bancin ra’ayi a hada kai a taimaki ‘yan uwa ‘yan gudun hijira, amma kiran sa keda wuya sai wani shehin darika yayi tsalle ya futar da wasu dattin maganganu ya jingina su ga Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam wanda ba a kansu ake magana ba, A’a sai dan kawai shi wannan shehin darika daya jin gina masa wannan datti, a tunani irin nasa hakan zai bata shi a Idon Al’umma, sai dai kash wannan malamin darika baiyi tunani ba domin kuwa mal ja’afar shekaru goma kenan cif-cif da rasuwar sa amma hakan har yanzu baisa shi yayi karatun ta nutsu ba, domin kuwa karatuttukan Mal Ja’afar har yanzu ba’a daina sauraron su a kafafe na yada sadarwa daban-daban ba,haka zalika duk da irin mutuwar da Mal Ja’afar yayi ashe hakan baisa ya zama darasi akan sa ya daina yin karyayyaki agareshi ba. Ba don komai yasa shi wannan malamin darika da sauran ‘yan uwansa ‘Yan Bidi’a ke kokarin yin batanci ga Mal Ja’afar ba sai don ya gagare su ta fuskar kawo hujjah a lokacin da yake raye dama yanzu da ba’a tare dashi a nan duniya amma kuma ana tare da muryar sa ta yada sunnah don kare Addinin Allah da sunnar Annabi Muhammad (S.A.W.) ,domin wannan shehin malamin darika har Mal Ja’afar ya rasu bai iya kare koda daya daga cikin abubuwan da suka shafi darikar sa ba idan ko har ta fuskar kafa Hujjah da Al’kur’ani da Ingatattun Hadisai ne sai dai kam idan ta fuskar labarai da tatsuniyoyi ne to wannan kam zai’iya tunda dama anan yafi kauri. Saboda haka malaman sunnah da dama sukan bada kariya ta fuskar hujjojin dake cikin al-kur’ani da ingatattun hadisai da maganganun sahabbai da tabi’ai duk lokacin da wani dan Bidi’a yayi kokarin cin mutuncin wani malamin sunnah a duk inda yake walau yana raye ko baya raye don haka ne ma Marigayi Sheikh Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria ya yiwa wata lecture sa take da Suna HABAA...SHEHI...!!! don saboda irin wannan maganganu da wannan shehin darika ya saba yiwa malaman sunnah musamman wadanda yaga basa raye tunanin sa babu wanda zai basu kariya. Sai dai ubangiji ta’ala yayi alkawarin kare addinin sa da wadanda suke yada shi, A wannan lokaci ma Allah ya bamu Ikon futo da Hujjojin malan Ja’afar daya bayyana da bakin sa kafin rasuwar sa don saboda irin wannan rana ta idan anga baka Raye azo ana maka karyayyaki akan abunda malami baiyi Fatawa akai ba kuma baya goyon bayan Da’awar hakan har ya koma ga ubangiji Ta’ala, wadannan Hujjoji kuwa sune Karatuttukan da Sheikh Ja'afar Mahmud Adam ya gabatar dan gane da halaccin karatun ilimin boko da aikin gwamnati, sabanin yadda wasu suke cewa haramun ne saboda haka wasu malaman Bidi'a suke amfani da wannan dama cewa ai shi ya kawo Da'awar Boko haram, ko yayi Fatawar hakan, to ga duk wanda ya saurari wadannan bayanai guda takwas zai tabbatar da cewa JI YA KORI A BAKA LABARI Domin sharri ne kawai na 'Yan Bidi'a da suke yiwa malan Ja’afar da sauran malaman sunnah, shi yasa wannan shafi ya sanya su don kafa hujjah ga masu jinginawa malan Ja’afar Da'awar haramcin karatun Boko ko Aikin gwamnati domin kuji da kunnuwan ku dannan link dake kasa daki bayan daki domin sauke su 01-A-Nunin Halaccin Karatun Boko http://darulfikr.com/s/24620 01-B-Nunin Halaccin Karatun Boko http://darulfikr.com/s/24621 02-A-Me Yasa suke cewa Karatun boko Haramunne http://darulfikr.com/s/24622 02-B-Me Yasa suke cewa Karatun boko Haramunne http://darulfikr.com/s/24623 03-A-Tafarki Madaidaici http://darulfikr.com/s/24624 03-B-Tafarki Madaidaici http://darulfikr.com/s/24625 04-A-ABinda Ake Kafa Hujja Dashi A Musulunci http://darulfikr.com/s/24626 04-B-ABinda Ake Kafa Hujja Dashi A Musulunci http://darulfikr.com/s/24627 Don haka nake bawa ‘yan uwa Ahlus-sunnah hakuri cewa sai munyi hakuri da maganganun da magauta ke yadawa dan gane da malaman mu domin yanzu Sunnah itace kasuwar ta take ci, Mafarki,Tatsuniya ,Kulunboto,da kwatance-kwatance Kasuwar su ta Daina ci, shi Yasa duk abunda ka fada za’a Tambaye ka Hujjah su kuma ‘Yan Bidi’a shi yasa abun ke basu haushi Kuma Yake Kona musu Rai domin basa iya kare Akidojin su. Don haka a shirye muke da mu bawa malaman mu na sunnah kariya walau suna raye ko basa raye ganin gudummawar da suke bawa Addinin Musulunci ba dare ba rana. Rubutawa:Hussaini Auwalu Ya’u Bita:Mubarak Auwal Da Taimakon : Basher Journalist Sharfadi Muhammad Basheer Ridwan Hassan Auwalu Ya’u Ammar Isah Hotoro Faisal Nasir Muhammad Kucigaba da kasancewa da Darulfikr.com domin samun karatukan malaman sunna a sawwake Darulfikr.com Takuce domin yada *Sunnah* © Copyright: Hussaini Auwalu Ya’u Facebook: https://fb.com/hussainiauwaluyau Instagram: hussainiauwaluyau01 Twitter: Hussainiauwalu1 Email: hussainyau01@gmail.com 05/shawwal/1438 A.h 29/ june /2017

by: Hussaini Auwalu Ya'u. · 530 · July 01, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853