SHIN ZAN IYA SAKIN AMARYATA DOMIN NA TARA DA ITA SAI NA GANE BABU BUDURCI A TARE DA ITA ???

Tambaya Assalamu alaikum malam amincin Allah ya kara tabbata ga malam tareda karin kariya har abada amin. Tambayata itace: Shin mutum nada hakkin sakin matarsa (Amarya) wacce ya aura ya tara da ita yagane cewa ba budurwabace akwai wani abu daya faru kafin tashigo gidansa. Zai iya sakinta? *Amsa* Wa'alaykumussalam Wannan na daga cikin shubuhohin aure wanda zargi ke kawo haka baya da tabbacin wani abu ya faru kafin ya aure ta, kuma koma wani abun ya faru ai tuba na kankare komai don haka yayi hakuri a cigaba da zama da matar sa, domin bincike ya nuna akwai hanyoyin da mace ka iya saryantar da budurcin ta koda bata sadu da wani da namiji ba... Don haka ya zauna da matar sa ya rike ta bisa amana. Wallahu A'alam *Amsawa*✍🏻 *Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed* 28/06/2017 Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

by: Mubarak Auwal · 2,955 · June 28, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853