TA YI ZINA, TANA TAKABA?

*_TA YI ZINA, TANA TAKABA!!!_* *Tambaya* Dr. Don Allah a yi mani Karin bayani akan hukuncin matan da take a cikin zaman iddar rasuwan miji (takaba) sai shaitan ya rinjayeta ta yi zina dai kuma ciki ya shiga kuma ta yi ikrari da bakinta cewa zina ta yi, shin za a iya jingina wannan dan ga mijin da ya rasu ko a'a? Allah ya yi maka jagora. *Amsa:* To dan'uwa tabbas wannan abin bakin ciki ne, ina rokon Allah ya kare mu daga zamewa, saboda yana daga cikin manufofin iddar takaba, kula da hakkin miji, duk matar da ta yi zina tana takaba, ba ta kula da wannan manufa ba, lokacin takaba lokaci ne na tuna miji, da nema masa gafara, da kuma neman kusanci da Allah, ba'a kwalliya a lokacin, ko da neman aure bai hallata ba ballatana kadaita da namijin da ba muharrami ba, balle har aka kai ga alfasha, tabbas ya kamata mu jin tsoron Allah. Ta aikata babban zunubi, kuma dan da aka samu, babu yadda za'a yi a danganta shi ga mamacin, tun da maganarka tana nuna bayan ya mutu ta samu cikin. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Zarewa.

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 3,636 · April 02, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853