HUKUNCIN KACIYAR MATA?

*HUKUNCIN KACIYAR MATA* Tambaya: Malan dan Allah ai mana bayani akan kaciyar Mata. Wai da gaske ne Manzo SAW yace a Yanke amma kadan? Da Allah inason cikakken bayani *Amsa*: Ya 'yar uwa hadisi ya tabbata wanda Abu dawud, Addabarany a cikin الأوسط ،da baihaqy a cikin الشعب , sun fitar da hadisi daga Ummu 'adiyyatil-ansaruyyah tace: wata mata a madina ta kasance tana yin kaciyar ( mata ), sai Annabi Alaihissalam yace da ita : " kar ki ringa yankewa da yawa ( ki yanke kadan ), domin hakan yafi rabautar da mace, yafi soyuwa ga miji" Imamul-Albany ya inganta wannan hadisin a cikin صحيح أبي داود. Haka nan Imamu Muslim ya fitar da hadisi daga Nana Aisha ,Allah ya qara mata yarda tace: Annabi Alaihissalam yace: " idan miji ya kwanta a tsakanin gabban matarshi hudu ( hannaye da kafafuwa ) ,sannan kaciyar ( miji) ta shafi kaciyar ( mace ), to wanka ya wajaba". Wannan hadisai da wasunsu suna nuni akan halascin kaciyar mace. An samu sabani tsakanin malamai dangane da hukuncin kaciyar mata, bayan gaba dayansu sun hadu akan halaccinta. Wasu malamai suna ganin wajibi ce kaciyar mata kamar yadda ta maza take, wannan shine ra'ayin shafi'iyya da Hanabila a zance mafi rinjaye na mazhabarsu. Da yawa daga cikin malamai sun tafi akan cewa ba wajibi bace kaciyar mata, sunnah ce da kuma cikar karamar mace, wannan kuma itace magana mafi dacewa, Mai son qarin bayani ya duba fatawar lajnatud-da'ima ,da fatawaa na bin bazz . Allah ne mafi sani. Anas Assalafy Fagge. 2/Rajab/1438 A.H Daga group din: *FATAWOWIN MATA*

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 3,762 · March 30, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853