MIJINA YANA CHARTING DA TSOHUWAR BUDURWARSA, BAYAN TA YI AURE?

*MIJINA YANA CHARTING DA TSOHUWAR BUDUWARSA, BAYAN TA YI AURE* *​Tambaya​* Assalamu alaikum. Allah ya taimaki Dr, mijina ne suke chat da wata matar aure, wadda tsohuwar budurwarsa ce a baya sama da shekara 20 da wani abu ta yi aure, suna turawa juna hotuna, shin malam wata shawara da nasiha ya kamata na yi masa? Sabo da kubutar da su ga fada wa halaka. Allah ya taimaki mallam ya kara fahimta. *​Amsa​* Wa alaikum assalam, Ki yi masa nasiha da tsoran Allah, sannan kuma ki nuna masa cewa: Inda matarsa ce ba zai so ayi irin wannan mua'malar da ita ba. Yin charting irin wannan da matar aure yana iya kaiwa zuwa zina, musamman da alama har yanzu kuna son juna, Allah ya hana duk abin da zai kusantar zuwa Zina a suratul Isra'a'i. Zunubi shi ne abin da ya maka kaikayi kuma ka ji tsoran kar mutane su yi tsinkayo akai. Wanda ya kiyaye Allah zai kiyaye Shi, wanda ya saba masa zai hadu da Shi a madakata. Dayanku ba zai yi cikakken imani ba har sai ya sowa dan'uwansa abin da yake soma kansa. Allah ne mafi sani. *​Amsawa​*✍🏻 *​DR.Jamilu Yusuf Zarewa*​ 27/3/2017

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 4,358 · March 27, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853