SHIN ZAN IYA KIRAN MAKIDA DA MAWAKA ALOKACIN BIKINA?

*SHIN ZAN IYA KIRAN MAKIDA DA MAWAKA A LOKACIN BIKINA...?* *19/3/2017* *TAMBAYA* Assslam alaika warahamatullah Allah ya karawa mallam lafia tambaya ta itace mallam bikin dana zaayi ya halatta na kira makada kokuma na kira masu kidan kwarya amma mata zalla zamuyi abinmu ? *AMSA* To yar uwa da farko dai shari'a ta bada dama lokaciin da ake biki ayi nishadi ayi yan wake wake kamar yadda an kawo nana Aisha Allah ya kara mata yarda da aka kawo ta gidàn Annabi S.A.W.sai Annabi yace ya naji kun taho shuru babu alamar biki harma Annabi S.A.W. ya fada musu abinda zasu dinga fada su matan da suka kawo nana Aisha Da wannan malamai suka ce babu laifi idan zaayi biki mata su danyi wake wake irin nasu mata wanda babu batsa ciki babu zambo sannan babu ainahin rawa ko fidda tsiraici sannan babu laifi malamai sunce a iya kada dumdufa a lokacin da akai aure ba laifi bane a shari'a domin alamar anyi aure a zamanin Annabi S..A.W shine ana kada wannan dumfa dumfa din a dan buga amma ba irin bugawar rawa ba da hannu ake bugewa kadan kadan Amma yanzu zamani yazo yahudawa da kafirai sun canja al'amuran sun shigo da ra'ayi da son zuciya da barna da irin abinda shari'a bata amince dashi ba Ina kira ga iyaye mata ya kamata ku sani cewa abinda kukeyi na gayyato makida maza karti ma ciya dawa a gayyoto su suzo cikin mata suna kida mata suna rawa da bayyana tsiraicinsu wannan haramun ne ba addini bane ya kamata kuji tsoron Allah Ku tsaya inda aka umarceku idan akwai mata masu kidan kwarya babu laifi ayi idan babu maganganu na batsa ko zambo ko maganganu irin na tada shaawa zaa iya yin kidan kwaryar amma ya zamana mata ne zalla babu namiji ko daya Allah shine mafi sani *Amsawa* *Dr Abdallah Gadon kaya*✍

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 1,881 · March 19, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853