ANGO YA MUTU KAFIN TAREWAR AMARYARSA YAYA BATUN GADO?

*ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA* ? 08/01/2016 *Tambaya* *Assalamu Alaikum* Malam dan Allah an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi? *Amsa* Wa'alaykumussalam, To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi (S.A.W). ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi . Allah shine mafi sani Amsawa Dr jamilu zarewa

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 1,422 · March 15, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853