ZAN IYA SALLAR NAFILA A LOKACIN TAFIYA

*_ZAN IYA SALLAR NAFILA  A LOKACIN TAFIYA?_* *Tambaya:* Assalamu alaikum, malam tambaya ta ita ce yaya hukuncin yin nafila yayin da mutum a halin tafiya wato yanayin kasaru, naji wasu malaman suna cewa ba'ayin nafila a yanayin kasaru don Allah malam ina bukatar amsa da gaggawa, nagode. *Amsa* wa alaikum assalam, To dan'uwa abin da aka rawaito idan Annabi S.A.W ya yi tafiya, yana barin nafiloli, in ba wutiri da raka'atanil fijr ba, kamar yadda Ibnul-kayyim ya ambata a littafinsa na Zadul-ma'ad 1\456. Wasu malaman suna ganin nafilolin da suke da alaka da sallolin farilla su ake bari, amma wadanda ba su da alaka da sallolin farilla kamar tsayuwar dare an iya yinta, an samu halaccin hakan daga Imamu Ahmad. Zadul-ma'ad 1\457. Allah ne Amsawa Dr jamilu yusuf zarewa

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 971 · March 01, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853