LOKACIN YAYE YARO A MUSULUNCI

*_LOKACIN YAYE YARO A MUSULUNCI._* *Tambaya:* Aslm ya shaikh :Allah yaqara wa doctur lafia amin. Don Allah mallam wane lokaci ne mafi inganchi da ya dace a yaye yaro daga barin shan nono a shariance? Nagode Allah yasaka da alkhairi amin. *Amsa:* To dan'uwa ina rokon Allah ya amsa addu'arka, Lokaci Mafi çıka na yaye yaro shı ne: idan ya kai shekaru biyu, kamar yadda aya ta: 233 a suratul Bakara ta tabbatar da hakan, saidai ya halatta a yaye yaro kafin ya cika shekaru biyu, mutukar ba zai cutu ba, kuma iyaye guda biyu sun cimma daidaito akan hakan.  Don neman karın bayani duba: Tafsirin Qurdubi 3/162. Allah ne mafi Sani. Dr. Jamilu Zarewa.

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 1,278 · February 26, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853