WAI ME YASA MUSULUNCI YA HANA MUSULMA AURAN CRISTA AMMA YA HALATTAWA MUSULMI AIRAN CRISTA?

*_WAI ME YASA MUSULUNCI YA HANA MUSULMA AURAN CRISTA, AMMA YA HALATTAWA MUSULMI AURAN CRISTA?_* *Tambaya* Malam wasu Arna ne suka mana tambaya a makaranta cewa: Yaya aka yi addinin musulunci ya halattawa namiji musulmi auran christer mace, amma ya hana a baiwa christer namiji auran musulma, malam mun rasa amsar da za mu ba su, shi ne muke so ka taimaka mana, don kar su samu hanyar da za su aibanta addininmu. *Amsa* To yar'uwa sheik Addiyya mohd Salim ya yi kokari wajan warware wannan mushkilar a karashen tafsirin Adhwa'ul-bayan da ya yi, inda ambaci dalilai guda biyu, wadanda suka hukunta hakan: 1. Kasancewar musulunci shi ne yake yin sama, amma ba'a yin sama da shi, idan christer ya auri musulma, zai zama yana sama da ita, tun da namiji shi ne yake bawa mace umarni, idan ya aure ta, sabanin idan namiji musulmi ne ya auri mace christer, tun da shi zai zama a samanta. 2. Musulmi ya yi imani da Annabi Isa da kuma Injila, wannan zai sa idan ya auri christer ya girmama ta, Shi kuwa christer bai yi imani da Annabi Muhammad S.A.W ba, don haka zai iya wulakanta musulma idan ya aure ta, tun da bai san darajar addinita ba, wanda hakan zai kai suka sa fahimtar juna, zaman auran ya ta'azzara. Duba Adhwa'ul-bayan 8/164. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Zarewa. 13/2/2015

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 904 · February 24, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853