INASON DALILIN AKAN KACIYAR MATA?

*_INA SON DALILI AKAN KACIYAR MATA?_* *Tambaya:* Assalamu alaikum, don Allah malam a taimaka min da amsar wannan tambayar, ko Qur'ani da hadisi sun yi Magana akan halarcin kaciyar mata, ko kuma wani daga cikin magabata na kwarai ya yi Magana akan haka? *Amsa* To 'yar'uwa akwai hadisai da suka zo akan cewa: mustahabbi ne, yin kaciyar mata, saidai an yi sabani akan ingancinsu, wasu malaman sun raunana su, wasu kuma sun inganta su. Baihaki a Sunanu Assugrah a hadisi mai lamba ta: 3712, ya rawaito mustabbacin yin kaciyar mata daga Ibnu Abbas da sanadi mai kyau. Hadisin da Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta a lamba ta: 108, daga Nana A'isha tana cewa: "Idan kaciya ta hadu da kaciya, to wanka ya wajaba" na nuna cewa : al'ada ne yiwa mata kaciya a zamanin Annabi (S.A.W) Ibnu- Abi-zaid Al-kairawany ya ambata a Risala shafi na: 410, cewa: yin kaciyar mata mustahabbi ne. Don neman Karin bayani duba Al-mugni 1\101. Allah ne mafi sani. Dr. Jamilu Zarewa. 12\5\2015

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 1,221 · February 24, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853