JINI NAWANE ISTIBRA'I?

*JINI NAWA NE ISTIBRA'I* *Tambaya:* Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa ne ISTIBRAI din ta? *Amsa:* To 'yar'uwa Allah ya haramta zina kuma ya sanyata daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba. Idan mazinaciya ta tuba, malamai sun yi sabani game da iddarta. 1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa za ta yı jini uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya wajaba ayı abin da zai tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita da kuskure za ta yi, da kuma wacce aka şaka. 2. Za ta yi jini daya kawai, saboda fadin Annabi S.a.w. "Ba'a saduwa da mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma sai ta yi haila daya" Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito. Don neman Karin bayani duba Almausu'a Alfikhiyya Alkuwaitiyya 30/341. Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana tabbata da jini daya, sannan iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya, saboda iddarta ana tsawaitata ne don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa babu shi a iddar zina. Allah ne mafi Sani. Dr Jamilu Zarewa 25/5/1438

by: Abu Abdirrahman Assalafy Kano · 1,044 · February 23, 2017

Darulfikr on Facebook

Like our page on facebook for daily updates. Darulfikr is your for propagation of Islam. Preach in Islam without been a scholar by sharing our fruitful updates to Muslim Ummah

For complaint, Suggestion or Advice +234 813954 5853